Shugaban tsagin jam’iyyar PRP na kasa, Farfesa Sule Bello, ya rasu

Ya rasu ranar Lahadi a Zariya, bayan fama da gaeruwar jinya.

Shugaban tsagin jam’iyyar PRP na kasa, Farfesa Sule Bello, ya rasu

PRP

Shugaban tsagin jam’iyyar PRP na kasa, Farfesa Sule Bello, ya rasu

Ya rasu ne ranar Lahadi a Zariya, Jihar Kaduna yana da shekara 73 bayan ya yi fama da gajeruwar jinya.

Wata majiya da ked a kusanci da mamacin ce ta tabbatar wad a Aminiya rasuwar tasa, inda ta ce za a yi jana’izarsa a gidansa da ke kan titin Maiduguri Road a unguwar Hotoro da ke Kano da karfe 4:00 na yammacin Lahadi.

Kafin rasuwarsa, shugaban dai malami ne a sashen Tarihi na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Kwana daya kafin rasuwar tasa, said a wata kungiyar matasa a Kano ta gayyace shi ya gabatar da makala a bikin cikar Najeriya shekara 61 da samun ’yancin kai, amma sai dai wani ya wakilce shi saboda rashin lafiyar.