Shugaban Tunisia Beji Caid Essebsi ya rasu
Rahotanni daga fadar shugaban kasar Tunisia ta sanar da mutuwar shugabanta Beji Caid Essebsi, wanda ya mutu yana da shekara 92. Beji ne shugaban kasar da ya fi kowa tsufa a duniya. An kwantar da shi a asibiti ranar Laraba amma jami’ai ba su fadi dalilin rashin lafiyar tasa ba. A shekerar 2014 ne Mista […]
Rahotanni daga fadar shugaban kasar Tunisia ta sanar da mutuwar shugabanta Beji Caid Essebsi, wanda ya mutu yana da shekara 92.
Beji ne shugaban kasar da ya fi kowa tsufa a duniya. An kwantar da shi a asibiti ranar Laraba amma jami’ai ba su fadi dalilin rashin lafiyar tasa ba.
A shekerar 2014 ne Mista Essebsi ya lashe zaben farko na kasa tun bayan boren kasashen Larabawa.
Mista Essebsi tsohon lauya ne da ya yi karatu a birnin Paris na Faransa. Ya kuma yi ministan harkokin cikin gida da kuma rike makamin kakakin majalisar wakilai.
Daga BBC