Shugaban Turkiyya ya ziyarci Najeriya
A shekaranjiya Laraba ne Shugaban kasar Turkiyya, Reccep Tayyip Erdoğan, ya kai ziyara Abuja, inda ya fara ziyaraNajeriya bayan ya baro kasar Ghana.Shugaban ya samu tarba daga wajen karamar Ministar Harkokin Waje Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim, da takwaranta na Birnin Tarayya, Mohammad Musa Bello da kuma jakadan Turkiyya a Najeriya, Hakan Çakıl.Daga nan ne […]
A shekaranjiya Laraba ne Shugaban kasar Turkiyya, Reccep Tayyip Erdoğan, ya kai ziyara Abuja, inda ya fara ziyaraNajeriya bayan ya baro kasar Ghana.
Shugaban ya samu tarba daga wajen karamar Ministar Harkokin Waje Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim, da takwaranta na Birnin Tarayya, Mohammad Musa Bello da kuma jakadan Turkiyya a Najeriya, Hakan Çakıl.
Daga nan ne sai Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya shiga gana wa da shi.
kasashen biyu sun tattauna a kan batutuwa da dama cikinsu har da tattalin arziki da tsaro.
Cikin wadanda ke yi wa Shugaba Erdoğan rakiya har da uwargidansa, Emine Erdoğan, da ministan harkokin waje, Meblüt Çabuşoğlu, da ta Muhalli, Fatma Güldemet Sarı, da na tattalin arziki Mustafa Elitaş, da na makamashi, Berat Albayrak, da na tsaro İsmet Yılmaz da kuma manyan ‘yan kasuwar kasar.
Alkaluma sun nuna cewa kasuwancin da ke tsakanin Najeriya da Turkiyya ya wuce na Dala biliyan biyu, kamar yadda BBC ta bayyana.
Hakazalika, kasashen na cikin kungiyar kasashe takwas masu ci gaba da kuma kasashen kungiyar MINT wato Medico da Indonesiya da Najeriya da kuma Turkiyya, wadanda ake hasashen tattalin arzikinsu zai bunkasa sosai nan da shekara 20.
Turkiyya dai tana da makarantu a Najeriya, cikinsu har da Jami’a da kwalejoji da dama.
Haka kuma Najeriya tana shigowa da darduma daga Turkiyya, yayin da ita kuma Turkiyya ke watsa labarai da harshen Hausa.