Shugaban Uganda ya jagoranci gangamin kin jinin ’yan luwadi da madigo

Shugaban kasar Uganda Yoweri Musebeni ya jagoranci wani bikin gangamin da aka shirya don yin maraba da dokar da ta haramta luwadi da madigo a kasar, inda ya ce mummunar dabi’ar na jawo cututtuka kuma ba ta dace da ‘yan afirka ba.Gangamin ya gudana ne a babban birnin kasar Kampala ranar Litinin da ta gabata. […]

Shugaban Uganda ya jagoranci gangamin kin jinin ’yan luwadi da madigo
Shugaban Uganda ya jagoranci gangamin kin jinin ’yan luwadi da madigo

Shugaban kasar Uganda Yoweri Musebeni ya jagoranci wani bikin gangamin da aka shirya don yin maraba da dokar da ta haramta luwadi da madigo a kasar, inda ya ce mummunar dabi’ar na jawo cututtuka kuma ba ta dace da ‘yan afirka ba.
Gangamin ya gudana ne a babban birnin kasar Kampala ranar Litinin da ta gabata. Wata dai kungiyar shugabannin addinan kasar da kuma wasu daga cikin jami’an gwamnatin ne suka dauki nauyin shirya bikin. Saboda su gode wa Ubangiji da kuma yaba wa Shugaban Musebeni, dalili da yadda ya bijire wa matsin lambar Yammacin Duniya kan dokar da ta haramta luwadi da madigo a kasar.
Dubbannin mutane ne suka halarci bikin gangamin cikinsu kuma har da yara ‘yan makaranta wandan da sukai ta rera wakokin kin jinin luwadi da ma na kin jinin Yammacin Duniya.
Shugaba Musebeni ya sanya hannu ne a dokar da ta haramta luwadi da madigo a watan Fabrairu. Dokar dai ta tanadi hukuncin daurin rai-da-rai ne ga duk wanda aka samu da laifin aikata mummunar dabi’ar. Shugaban ya ce ya shirya tsaf don yakar ‘yan luwadin Yammacin Duniya saboda yadda suke taimaka wa yaduwar mummunar dabi’ar a kasashen Afirka. Matakin sanya dokar dai, ya sa Uganda cikin jerin kasahen Afirka 37 da suka haramta luwadi da madigo.
Amma tun bayan sanya dokar ne kuma, kasar ta Uganda ta fara fuskantar suka daga kungiyoyin kare Hakkin Bil’adama da kasashen duniya da ke goyon bayan ‘yan luwadi da madigo. Inda suke bayyana cewa dokar ta yi tsauri sosai.
A matakinsu na adawa da dokar, kasashen Yammacin Duniya sun dakatar da tallafin Dala miliyan 118 da suke ba Uganda, a fatansu na ganin kasar ta yi watsi da dokar.
kasar Uganda dai ta dogara da tallafin kudin da take samu daga kasahen Yamma ciki har da kudin da ake ba ta don cike gibin kasafin kudinta. Amma a baya akwai lokacin da kasashen Yamma suka taba dakatar da tallafin (a cikin shekarar 2013), saboda zargin cin-hanci-da-rashawa da ake wa jami’an gwamnatin kasar. A lokacin kasar ta samu koma baya amma kuma tattalin arzikin kasar ya bunkasa da kashi 6 cikin dari.
A martaninsa kan janye tallafin, Shugaban Ugandan ya ce: “Ba ma bukatar kudadensu saboda kasarmu na daya daga cikin kasashe masu arziki a duniya. Za su janye tallafin kudaden da suke ba mu ne sakamakon adawa da suke yi da wannan dokar, amma Uganda za ta rayu ba tare da su ba.” Inji shi
An fara gabatar da kudirin dokar ne cikin shekarar 2009 bayan da wani dan majalisar kasar mai suna Dabid Bahati ya bukaci hakan, inda ya gabatar da bukatar hukuncin kisa ga wanda aka kama da laifin karya dokar musammam ma idan yana dauke da cutar nan mai karya darkuwar jiki(HIb). Amma a lokacin da ta zama doka sai aka yi sassauci zuwa hukuncin daurin rai-da-rai.
A lokacin da kudirin ya zama doka ne, kasar Amurka ta bayyana dokar da “wani danyan aiki” kuma ta ce za ta kara waiwayar dangantakarta da kasar. Majalisar Tarayyar Turai ma ta goyi bayan matakan takunkumin da aka sanya wa Uganda kan dokar, inda ta ce dokar ta take hakkin dan Adam da kuma ‘yanci ‘yan kasar a damukradiyance.