Shugaban Ukraine ya nemi tallafin Najeriya a yakinsu da Rasha
Ya ce ya kamata kasashen Afirka su tallafa musu a kawo karshen yakin
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya nemi tallafin Najeriya, Kwaddibuwa da ma sauran kasashen Afirka kan yakin da kasarsa ke gwabzawa da Rasha.
Zelenskyy ya ce tuni ya tattauna da shugabannin kasashen biyu da ma wasu na Afirka a kokarinsa na gina alakar tattalin arziki a tsakaninsu.
- Tarar N5m: Saboda al’umma muka yi rahoto kan ’yan bindiga – Trust TV
- Biranen Amurka 2 sun fara buga takardar kada kuri’a da Larabci
A yayin wani taron manema labarai ta intanet ranar Alhamis, shugaban ya ce jarin da Ukraine ta zuba a kasashen Afirka zai habbaka tattalin arzikinsu sannan ya inganta samar da abinci.
Ya ce, “Mun yi waya da shugabannin Najeriya da na kwaddibuwa da ma na wasu da dama. Na yi amannar duk da yanayin yakin da muke ciki, ya kamata mu gina kyakkyawar alakar cinikayya a tsakaninmu. Yana da matukar wahala daga bangarenmu, amma ina son kasashen Afirka su hada kai su samar wa kansu mafita a fannin samar da abinci.
“Yanzu haka ba za mu iya shiga kasuwannin Afirka ba saboda Rasha ta toshe ko ina, amma duk da haka na tabbata akwai karin hanyoyin cinikayya da za mu iya amfana da su,” inji Zelenskyy.
Da aka tambaye shi nan da yaushe yake hasashen yakinsu da Rasha zai iya karewa, sai ya ce hakan ya danganta ne da lokacin da duniya ta tallafa musu.
A cewarsa, “Matukar Putin ya ki mika wuya, za a fuskanci matsalar karancin abinci, kuma hakan zai shafi zaman lafiyar duniya baki daya. Ba mu muka fara yakin nan ba, amma mu za mu kawo karshensa.
“A matsayina na Shugaban Kasar Ukraine, na yi kiran a tattauna a lokuta da dama, amma sun riga sun yanke shawarar mamaye mu, su kashe mu. Ba za mu bari hakan ta ci gaba da faruwa ba. Ina ganin ya kamata kasashen Afirka su taru su tallafa wa Ukraine.”