Shugaban ’yan daban Yobe ya shiga hannun hukuma

Ya amsa laifukan da ake zargin sa na kasancewa shugaban ’yan daba da kuma addabar al’ummar Jihar Yobe

Shugaban ’yan daban Yobe ya shiga hannun hukuma

’Yan sanda sun kama shugaban ’yan daban da ke addabar Jihar Yobe, Haruna Mohammed da wasu ’yan kungiyar asiri.

Kwamishinan ’Yan Sandan Yobe, Garba Ahmed, ya sake jaddada cewa babu wata maboya ga masu aikata laifuka a jihar, walau a birni ko a karkara.

Kwamishinan ’yan sandan ya bayyana cewa jami’an leken asiri na jihar (SID) sun kama Haruna Mohammed, dan shekara 40 ne a kauyen Lantewa da ke Karamar Hukumar Tarmuwa.

Haruna Mohammed dai shugaban gungun ’yan daba ne wanda ya ƙware wajen neman kuɗi  ta hanyar yin barazana ta wayar tarho, inda yake barazanar kisa, ko lahani ga duk wanda suke so su cuta.

Kwamishinan ’yan sandan ya kara da cewar, rundunar ta dade tana bin diddigin Haruna Mohammed kan yadda yake da hannu a ta’addanci a garuruwa, kauyuka, da jihohi makwabta.

Wani wanda abin ya taba fadawa a hannun Haruna a Karamar Hukumar Tarmuwa, ya ce shugaban ’yab daban ya bukaci Naira miliyan daga wajensa tare da barazanar kashe shi da iyalinsa idan ya ki ba da kudin.

A ranar 16 ga watan Yuni, 2024, da misalin karfe 1415 na safe, jami’an  SID, a wani samame na hadin gwiwa, suka kama Haruna  Mohammed a kauyen Nangillam, karamar hukumar Tarmuwa.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce Haruma ya amsa laifukan da ake zargin sa da aikatawa.

Rundunar ta kara da cewa ta yi nasarar  kama wasu ’yan kungiyar asiri, wadanda a halin yanzu suke amsa tambayoyi.

Don haka kwamishinan ’yan sandan ya yi gargadin cewa duk wanda ke da dabi’ar aikata laifi zai yaba wa zaki a hannun rundunar.

Ya kuma bukaci al’umma da su kai rahoton duk wani nau’in hare-haren, ko yunkurin aikata laifi ga ’yan sanda tare da yin kira da a ba su cikakken goyon baya domin tabbatar da tsaro a jihar.