Shugaban ’yan gwangwan ya nemi tallafin gwamnatin Jihar Edo
Shugaban kungiyar masu sana’ar saye da sayar da kayan bola da aka fi sani da ’Yan Gwangwan, reshen Jihar Edo, Alhaji Abbas Garba ya ce kungiyarsu tana taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa kasar nan, don haka ya bukaci gwamnatin Jihar Edo da ta Tarayya su tallafa musu domin su samu tafiyar da ita cikin […]
Shugaban kungiyar masu sana’ar saye da sayar da kayan bola da aka fi sani da ’Yan Gwangwan, reshen Jihar Edo, Alhaji Abbas Garba ya ce kungiyarsu tana taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa kasar nan, don haka ya bukaci gwamnatin Jihar Edo da ta Tarayya su tallafa musu domin su samu tafiyar da ita cikin nasara.
Shugaban ya yi wannan furucin ne a wata zantawa da Aminiya a garin Benin, Jihar Edo a cikin wannan mako. Ya ce: “Duk da irin matsaloli da muke fuskanta a wasu lokutan a bangaren hukuma a kan wannan sana’a amma kuma alhamdulillahi, muna samun abin biyan bukatar kanmu da na iyalanmu.”
Ya kara da cewa: “Kuma kamar yadda na ce, akwai matsaloli da dama da muke fuskanta a cikin wannan sana’a, domin wasu lokutan idan muka bai wa yaran gidanmu kudi don su je su nemo su sayo wannan kaya, idan suka yi karo da zauna gari banza sai su yi musu barazana, su karbe kudin daga hannunsu. Wasu lokutan kuma daga kananan ma’aikatan gwamnati matsalar take, domin idan suka raina kurwarka kai dan gwangwan, take sai su wulakanta ka, su dora maka sata kuma haka lamarin yake idan muka loda wannan kayan zuwa wani gari ko wata jihar. Ma’aikatan hanya suna matsa wa ’yan kasuwarmu sai mun biya su makudan kudi da suka zarce ka’ida.”
Shugaban ya ce wannan dalilin ne ya sa yake rokon gwamnatin Jihar Edo da ta Tarayya su tallafa wa san’ar tasu, yadda za su samu karfin gudanar ita ciki da waje kuma wannan zai taimaka wajen rage yawan zaman kashe wando ga wasu matasan kuma zai taimaka wa kasar nan a bangaren tattalin arziki.
Da yake kare batun zargin da ake yi wa yarasu na kwasar tukwanen mata da kwanuka, sai ya ce: “Wannan kage ne kurum, babu kanshin gaskiya a ciki, domin mu ba mu aikensu su je su sace tarkacen jama’a. Baicin haka muna tantancewa kafin mu dauke su su fara aiki da mu kuma muna sa musu ido tare da ja musu kunne a kan kada su yarda su taba kayan mutane. Wannan shi ne abin da ni na sani.”