Shugaban ’yan Ombatse ya ki bayyana a gaban kwamiti kan dalilan tsaro

Baba Alakyo mutumin da aka hakikance shi ne shugaban addini na al’ummar Eggon da ake zargi da kashe jami’an tsaro a ranar 7 ga Mayun da ya gabata a garin Alakyo da ke Jihar Nasarawa ya ki halartar zaman kwamitin binciken lamarin a ranar Litinin da ta gabata, inda lauyansa ya alakanta hakan kan dalilai […]

Shugaban ’yan Ombatse ya ki bayyana a gaban kwamiti kan dalilan tsaro

Umaru Tanko Al-Makura Gwamnan Jihar NasarawaBaba Alakyo mutumin da aka hakikance shi ne shugaban addini na al’ummar Eggon da ake zargi da kashe jami’an tsaro a ranar 7 ga Mayun da ya gabata a garin Alakyo da ke Jihar Nasarawa ya ki halartar zaman kwamitin binciken lamarin a ranar Litinin da ta gabata, inda lauyansa ya alakanta hakan kan dalilai na tsaro.
A ranar Juma’ar makon jiya bayan Gwamnan Jihar Umaru Al-Makura ya bayyana a gaban kwamitin sai shugaban kwamitin Mai shari’a Joseph Gbadeyin ya ce ana sa ran Baba Alakyo ya bayyana a gaban kwamitin ranar Litinin. Sai dai kuma shugaban kwamitin da wakilansa sun halarci wurin zaman suka yi jira daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma ba tare da Baba Alakyo ya bayyana ba, lamarin da ya tilasta dage zaman kwamitin zuwa Litinin 4 ga wamba bisa sa ran bayyanarsa a ranar.
Kafin nan Sarkin al’ummar Eggon Arren Eggon Bala Angbazo ya ce shugaban kungiyar Ombatse Baba Lakyo ba zai bayyana a gaban kwamitin ba, lokacin da mambobin kwamitin a karkashin Mai shari’a Joseph Gbadeyan suka ziyarce shi a fadarsa da ke Nasarawa Eggon.
Ya ce in ban da fadarsa Baba Lakyo ba zai bayyana a gaban wani ba. Ya ce “Idan kuna so ku ga Baba Lakyo ko a yau za ku iya ganinsa. Amma a nan fadata don shi mutumin Eggon ne.”
Kan matakin da ya dauka game da rikicin da ya auku a kauyen Alogani da ke yankinsa kwanakin baya, ya ce bayan aukuwar lamarin Gwamna Umaru Al-Makura ya je kauyen, kuma ya ziyarce shi a fadarsa inda suka tattauna kan lamarin, a karshe ya yi alkawarin zai dawo su dauki matakin da ya dace amma har yanzu bai ga Gwamnan ba balle ya san mataki da za su dauka.
Tun farko Mai shari’a Gbadeyan ya shaida wa basaraken cewa, “Mun zo ne mu nemi hanyoyi da shawarwarin da za su taimaka wajen kawo karshen tashin-tashina a jihar.”
Ya ce sun tuntubi wasu fitattun mutanen Eggon a jihar nan da kasa baki daya kan su taimaka shugaban kungiyar Ombatse ya bayyana a gaban kwamitin don akwai wasu tambayoyi suke son yi masa, game da kisan jami’an tsaro da aka yi a kauyen Lakyo a kwanakin baya, amma shiru. “Saboda haka ne muka tuntunbe ka a matsayinka na Sarkin al’ummar Eggon ka sa baki Baba Lakyo ya bayyana a gaban kwamitin.”  Ya ba da tabbacin cewa babu abin da zai faru da Baba Lakyo idan ya bayyana a gaban kwamitin.
Daga bisani Basaraken ya bukaci mambobin kwamitin su ba shi lokaci ya tuntunbi sauran shugabannin al’ummar Eggon a jihar game da batun kafin ya sanar da su matakin da suka dauka.
A lokacin da kwamitin ya ziyarci Gwamna Al-Makura a gidan gwamnati don jin na bakinsa game da zargin da Sarkin Eggon ya yi masa, Gwamnan ya ce kodayake ya ziyarci kauyen Alogani bayan rikicin amma bai yi wa Sarkin Eggon alkawarin zai same shi don su tautauna wani abu da ya shafi lamarin ba.
Kuma ya karyata zargin da babban lauyan Ombatse Barista Zakariya Alumaga ya yi a takardarsa cewa Gwamnan ne yake daukar nauyin harkokin kungiyar Ombatse, inda ya ce bai da wata alaka da ita.