… Shugaban ’Yan sanda na neman yi wa EFCC gyaran fuska

Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Solomon Arase, ya rubuta wa Hukumar EFCC takardar niyyarsa ta janye dukkan ’yan sandan da suka kai shekara biya a hukumar.Jaridar Premium Times da ke fitowa a intanet ta ce wata majiya mai tushe a hedkwatar ‘’yan sandan da ke Abuja ta shaida mata haka.Jaridar ta fadi a jiya […]

… Shugaban ’Yan sanda na neman yi wa EFCC gyaran fuska
… Shugaban ’Yan sanda na neman yi wa EFCC gyaran fuska

Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Solomon Arase, ya rubuta wa Hukumar EFCC takardar niyyarsa ta janye dukkan ’yan sandan da suka kai shekara biya a hukumar.
Jaridar Premium Times da ke fitowa a intanet ta ce wata majiya mai tushe a hedkwatar ‘’yan sandan da ke Abuja ta shaida mata haka.
Jaridar ta fadi a jiya Alhamis cewa a cikin wata takarda mai lamba CB/33/80/IGP.SEC/Abj/bol.52/60, dauke da kwanan 14 ga Yuli, 2015 Arase ya umarci EFCC ta tattaro sunan dukkan jami’an bisa mukamansu tare da mika wa ofishinsa cikin gaggawa.
Majiyar jaridar ta ce, idan aka aiwatar da umarnin zai shafi manyan shugabanni da masu bincike a hukumar – ciki da shugaban na EFCC – wanda shi ma ya shafe fiye da shekara biyar a hukumar.
A daukacin zaman Lamurde a hukuma ya shafe shekara 12, inda ya fara da Daraktan Ayyuka a a shekarar 2003 a zamanin shugabancin Nuhu Ribadu, kafin a nada shi shugaban riko a Janairun 2008 bayan cire Ribadu.
Ya mika wa Farida Waziri a Mayun 2008, inda aka sake nada shi Daraktan Ayyuka na hukumar a Disamban 2010.
Kuma ana cire Farida Waziri a watan Nuwamban 2011 aka sake nada shi shugaban riko na hukumar kafin a tabbatar masa da shugabancin hukumar a Fabrairun 2012.
Jaridar ta ce, yayin da aka kasa gano manufar Arase na sauya jami’an wasu majiyoyi sun ce wadannan manyan janye jami’ai zai raunana ayyukan EFCC musamman a yanzu da ta farfado da yaki da cin hanci da rashawa.
Sai dai kakakin ’yan sandan Najeriya, Emmanuel Ojukwu, ya ce bai da masaniya kan wancan wasika. Amma ya tabbatar da ana sauye-sauye wa jami’an ’yan sanda a hukumomi da dama ciki har da EFCC da sauransu kamar yadda aka saba.
 “Wadanan sauye-sauyen wurin aiki da Sufeto Janar ke yi ana yi ne don ba jami’an damar dada kwarewa,” inji Ojukwu
Da aka tambaye shi ko manufar sauyin wurin aiki shi ne a raunana hkumar sai ya ce: “Wannan zancen banza ne. kowane dan sanda mai bincike ne kuma kowane dan sanda zai iya aiki a ko’ina.”
Ya ce sauye-sauyen aiki na iya aukuwa a kowane lokaci idan shugaban ’yan sandan ya bayar da umarni.
Kakakin Hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce ba a yi masa bayani kan umarnin na Sufeto Janar ba, inda ya yi alkawarin zai bincika tare da tuntubar jaridar ta Premiuim Time, sai dai ta ce har zuwa buga rahotonta bai yi haka ba.