Dan sandan da ya ki karbar cin hancin Dala 200,000 ya Musulunta a Kano

Amah, ya yi alƙawarin neman ilimin addini tare da ci gaba da yi wa al’umma hidima.

Dan sandan da ya ki karbar cin hancin Dala 200,000 ya Musulunta a Kano

Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda da ya yi fice wajen kwatanta gaskiya da amana, ACP Daniel Amah, ya karɓi Addinin Musulunci a Fadar Sarkin Kano.

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ne, ya jagoranci musuluntar da shi tare da sanya masa sabon suna, Muhammadu Sanusi.

Sarkin ya yi kira ga Mista Amah da ya zurfafa iliminsa na addinin Musulunci, ciki har da koyon yadda ake salla, azumi, da bayar da zakka.

Haka kuma, ya shawarce shi da ya ci gaba da girmama iyayensa, duk da bambancin addininsu, tare da riƙe kyawawan halayensa.

Sunan Mista Amah, ya yi amo a watan Afrilun 2022 bayan ya ƙi karɓar cin hancin dalar Amurka 200,000 da wasu ’yan fashi suka ba shi.

’Yan fashin sun sato kuɗi sama da Naira miliyan 300, amma daga bisani suka shiga komarsa.

Wannan hali nasa na riƙon gaskiya ya sa aka ɗaga darajarsa zuwa Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda a watan Nuwamban 2022.

Da yake magana kan dalilin da ya sa ya karɓi Addinin Musulunci, Mista Amah ya bayyana godiyarsa bisa kyakkyawar tarba da ya samu.

Ya yi alƙawarin riƙe gaskiya, adalci, da ci gaba da yi wa al’umma hidima.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa