Shugaban Zambiya ya sallami mataimakinsa farar fata

A ranar Litinin da ta gabata ne Sabon Shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu ya sallami Mataimakin Shugaban kasar Guy Scott, wanda ya kansance shugaba farar fata na farko a nahiyar Afirka. Mista Scott ya zama shugaban rikon kwaryar kasar ne bayan rasuwar Shugaba Michael Sata a watan Oktoban bara. Wannan ya sa ya zama shugaba […]

Shugaban Zambiya ya sallami mataimakinsa farar fata
Shugaban Zambiya ya sallami mataimakinsa farar fata

A ranar Litinin da ta gabata ne Sabon Shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu ya sallami Mataimakin Shugaban kasar Guy Scott, wanda ya kansance shugaba farar fata na farko a nahiyar Afirka.

Mista Scott ya zama shugaban rikon kwaryar kasar ne bayan rasuwar Shugaba Michael Sata a watan Oktoban bara. Wannan ya sa ya zama shugaba farar fata na farko a nahiyar tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudu, kimanin shekara 20 da suka wuce.
An maye gurbin Mista Scott ne da Misis Inonge Wina, wacce tsohuwar minista ce kuma shugabar mata a jam’iyyar Patriotic Front. Kuma bayan mutuwar Shugaba Sata ne Mista Scott ya sallami Mista Lungu daga mukamin sakatare janar din jam’iyyarsu, amma daga bisani an mayar da shi kujerar bayan wasu masu zanga-zanga sun bukaci haka.
Mista Scott wanda dan asalin kasar Scotland ne. Kodayake, kundin tsarin mulkin kasar ya hana shi tsayawa takara a zaben da aka gudanar makon jiya saboda iyayensa ba haifaffun kasar Zambiya ba ne.
Har ila yau, sabon Shugaban kasar ya yi sauye-sauyen ministoci bayan ya lashe zaben na makon jiya, amma ya bar Ministan Kudin kasar Aledander Chikwanda da na Harkokin Wajen kasar Harry Kalaba. Mista Lungu shi ne tsohon ministan tsaron kasar. Kuma zai kammala wa’adin Shugaba Sata da ya rage ne. Kuma wa’adin zai kare ne a watan Satumbar badi.