Shugabanci daga Allah ne

A wannan mako, ina so ne mu yi wa Ubangiji Allah Madaukakin Sarki godiya domin irin alheri da jin kai da Ya nuna mana a zamanmu na ’yan kasar Najeriya. Idan ba domin alherin Allah ba; gaskiya ba za mu taba sanin wani yanayi muke ciki a yanzu ba. Kafin zaben da ya gabata; mutane […]

Shugabanci daga Allah ne
Shugabanci daga Allah ne

A wannan mako, ina so ne mu yi wa Ubangiji Allah Madaukakin Sarki godiya domin irin alheri da jin kai da Ya nuna mana a zamanmu na ’yan kasar Najeriya. Idan ba domin alherin Allah ba; gaskiya ba za mu taba sanin wani yanayi muke ciki a yanzu ba. Kafin zaben da ya gabata; mutane masu bi da dama mun yi ta yin addu’a domin Allah Ya ba mu zaman lafiya cikin wannan kasa game da zaben shugabanni a cikin wannan kasar; godiya da daukaka su tabbata ga shi Ubangijinmu da mai cetonmu Yesu Kiristi wanda yake amsa addu’o’in bayinsa, Allah dai Ya ba mu nasara cikin wannan zabe. Sai mu ce wa Allah Ubangijinmu MUN GODE!!

A cikin Littafin Romawa 13:1 – 5; maganar Allah tana cewa “Bari kowane mai rai shi yi zaman biyayya da ikon masu mulki; gama babu wani iko sai na Allah, ikon da ke akwai kuma sanyayyu ne na Allah. Wanda ya yi tsayayya da iko fa, yana tsayayya da umarnin Allah ke nan; masu tsayayya kuwa za su jawo wa kansu hukunci. Gama masu mulki ba abin tsoro ba ne ga aikin nagarta, sai ga na mugunta. Kana so ka zauna da rashin tsoron iko fa? Sai ka yi abin da ke nagari, za ka samu yabo kuwa daga gare shi; gama shi mai hidimar Allah ne a gare ka zuwa nagarta. Amma idan kana aikata mugunta, ka ji tsoro; gama ba kawai yake rike da takobi ba: gama shi mai hidimar Allah ne, mai ramawa da fushi ne a kan mai aikata mugunta. Domin wannan fa ya wajaba a gare ku, ku yi zaman biyayya, ba domin fushi kadai ba, amma sabili da lamiri kuma.”
Haka nan kuma cikin Littafin 1Bitrus 2 : 13 – 17 maganar Allah tana cewa; “Ku yi biyayya ga kowane hukunci na mutane sabili da Ubangiji: ko ga sarki, wato na birbishin doka ne; ko kuwa ga masu mulki, wato aikakkunSa ne domin ramawa bisa masu aikata mugunta, da yabo ga masu aikata nagarta. Gama haka nan nufin Allah yake, bisa ga aikin kirki ku kwabe jahilcin mutane marasa hikima; kamar ’yantattu, ba kuwa za ku mori ’yancinku kamar mayafin keta ba, amma kamar bayin Allah ne. Ku girmama dukan mutane, ku kaunaci ’yan uwanci, ku yi tsoron Allah, ku girmama sarki.”
Ina so mu gane wasu abubuwa masu muhimmanci sosai idan ya zo ga shirin Allah ga zaben shugaban al’umma;
Babu wani iko sai na Allah: Ko mene ne ra’ayin mutum sai mu sani, cewa mulki daga wurin Allah yake; lallai ne za ka iya zama da naka ra’ayi na siyasa, amma sai ka san wannan; duk abin da Allah Madaukakin Sarki Ya yarda Ya kuma bari ya faru, ya zama nufinsa wancan abin ya kasance a daidai wancan lokaci. Ya kamata ne kowane dayanmu ya yi na’am da dukan sakamakon zabe; domin mai yiwuwa, nufin Allah ne. Maganar Allah na cewa babu wani iko sai na Allah.
Dukan masu mulki sanyayyu ne na Allah: Mutum ba shi da ikon sa wani mutum bisa mulki. Yardar Allah ne kadai yakan sa mutum shi hau ragamar mulki a ko’ina. Ina so ne in jawo hankalin kowa da kowa ga wannan. Mun yi zabe bai dade ba na shugabanni a matsayi daban-daban, har zuwa ga zaben Shugaban kasa, Allah cikin alherinSa Ya sa Janar Muhammadu Buhari ya ci wannan zabe, sai kowa ya san cewa Allah ne Ya sa shi zai yi shugabanci na tsawon lokacin da Allah Ya ba shi, domin wannan duk wanda ya yi tsayayya da shi a matsayin shugaban kasanmu; yana tsayayya ne da umarnin Allah. Ya zama dole ne mu taimake shi da addu’a domin shi Ubangiji Allah Ya taya shi rikon wannan amana.
Dukan masu shugabanci masu hidima ne na Allah: Kamar yadda Pastor mai hidima ne a cikin Ekklisiyar Almasihu, haka kowane mutum da Allah Ya dora shi bisanka a matsayin shugaba, ya zama mai hidima ne a gaban Allah, ko shi mai bin Yesu Kiristi ko kuwa ba mai bin Yesu Kiristi ba. Allah Shi ke rike da zuciyar kowane mai mulki, Shi kadai ke da ikon jawo tunanin shugaba ga yin adalci. Shugabanci– yin aikin Allah ne.
Dole ne mu yi zaman biyayya: Wannan umarnin Allah ne, Allah Ya rigaya Ya ba wa kowane mutum da yake mulki ikon hukunta laifi, ko kuwa mugunta, idan mun gane cewa Allah ne Ya sa kowane shugaba bisa mulki, yin biyayya ga maganarsa wadda take daidai da nufin Allah; zai zama kamar yi wa Allah biyayya ne da yake Shi ya sanya shi bisa ragamar mulki.
Dole ne mu ba su girma: A wannan kasa tamu Najeriya, mutane da yawa sun saba zagin shugabanni, wani lokaci ma babu wani dalili cikakke, irin wannan hali ba hali mai kyau ba ne ko kadan, mu darajanta shugabanninmu, mu ba su girman da ya cancanta.
Mu ci gaba da yi musu addu’a domin su ci nasara: Maganar Allah tana koya mana a cikin Littafin 1Timothawus 2: 1 – 3, da cewa “A farkon farawa dai, ina umarni a yi bide-bide da addu’o’i da roke-roke da godiya, sabili da dukan mutane; domin sarakuna da dukan wadanda suke manya domin mu yi ranmu mai natsuwa da hankali kwance cikin dakin ibada da kimtsa fuska. Wannan mai kyau ne, abin karba kuwa ga Allah mai cetonmu shi wanda yake nufi dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” Idan har muna so mu yi rayuwa da ta dace a gaban Allah, ya zama dole ne mu taya masu rikon mulki da addu’a domin su iya cin nasara. Masu iya magana sukan ce, “Na Zaune gwanin kokawa” wani lokaci sai mu ga kamar idan da mu ne a wurin da za mu yi shi da kyau fiye da shi wanda yake wurin a yanzu; gaskiyar kuwa ita ce, idan ka shigo wurin, ba wuya ba za ka iya yin komai ba, za a gwammace wanda yake wurin kafin kai, asiri daya na cin nasara shi ne rokon Allah cikin addu’a.
Muna shiga sabon fage ne yanzu a matsayin mu na kasa; jama’a, kamar yadda muka yi addu’a ga shi shugabanmu na yanzu domin ya ci nasara a cikin shugabancin wannan babbar kasa – Mai girma Goodluck Ebele Jonathan; wanda a cikin kwanaki kadan masu zuwa zai sauka daga mulkin wannan kasa, haka nan dole mu bada goyon baya cikin addu’o’i ga shi Mai girma Janar Muhammadu Buhari yayin da zai karbi shugabancin wannan kasa nan da kwanaki kadan masu zuwa; da fatan Ubangiji Allah zai ba shi hikima da basira ya iya cin nasara a wannan lokaci da Allah Ya ba shi zarafi.
Kada mu fasa yin godiya ga Allah wanda Ya sa aka soma cin nasara cikin yakin da muke fuskanta a yanzu, mun gode wa Allah domin mata da dama da aka kubutar da su daga dajin Sambisa da fata sauran ma Allah cikin alherinSa zai sa a same su, amin.