Shugabanci: Muhimmancin bayyana kadarori a bainar jama’a

Tun kafin hawa ragamar mulki da kwana daya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa, Yemi Osinbajo suka bayyana kadarorinsu a rubuce ga Hukumar Kula Da da’ar Ma’aikata (CCB), kamar yadda Babi na bI, Sashi na 140 na Kundin Tsarin Mulki ya tanadar, inda aka ce: “Mutumin da aka zaba a matsayin Shugaban kasa ba zai […]

Shugabanci: Muhimmancin bayyana kadarori a bainar jama’a
Shugabanci: Muhimmancin bayyana kadarori a bainar jama’a

Tun kafin hawa ragamar mulki da kwana daya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa, Yemi Osinbajo suka bayyana kadarorinsu a rubuce ga Hukumar Kula Da da’ar Ma’aikata (CCB), kamar yadda Babi na bI, Sashi na 140 na Kundin Tsarin Mulki ya tanadar, inda aka ce: “Mutumin da aka zaba a matsayin Shugaban kasa ba zai kama aikinsa na ofishin shugabanci ba har sai ya bayyana kadarori da basussukansa da ya mallaka.” Haka kuma, ita kanta hukumar ta CCB, tuni ta tabbatar da amsar wadannan bayanai daga shugaban da mataimakinsa a rubuce.

Tun daga lokacin ne kuma ake ta takaddama, inda mutane ke gardandamin ko wannan abu da shugaban kasar ya yi, ya yi daidai da alkawarin da ya dauka a lokacin da yake yakin neman zabe, inda ya ce zai bayyana kadarorinsa karara ga bainar jama’a? Ita kanta hukumar CCB ta ce ba ta da ikon bayyana kadarorin nasu ga bainar jama’a “a yanzu’” kuma shugaban hukumar, Mista Sam Sada ya ce Majalisar Tarayya ce kadai za ta iya yanke manufar takardun bayanan, ko zai yiwu a bayyana su ga al’umma.
“A yayin da Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya da Dokokin Hukumar Kula Da da’ar Ma’aikata suka ba hukumar karfi da ikon amsar bayanan kadarorin da tantance su, bincikar su, adana su da kuma bin kadin an gudanar da binciken ko an samu daidaito da zahirin abin da aka bayyana, hakkin gane ko zai yiwu kuma ta yaya za a bayyana su ga al’umma, yana hannun Majalisar Tarayya.” Inji shi.
Irin yadda aka yi ta samun kwarmato da cece-kuce, musamman daga ’yan adawa game da al’amarin nan, lallai bai kamata a kawar da kai haka nan ba. Shi kansa mai magana da yawun Shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya ba al’ummar kasa tabbacin cewa a tsakankanin kwanaki dari na farko za a bayyana kadarorin shugabannin, bayan Hukumar Kula Da da’ar Ma’aikata ta gama bincikenta a kan takardun bayanan da aka gabatar mata.
A ganinmu, ba mamaki abin da ya kawo tsaiko ga Shugaban kasa ya ida cika alkawarin da ya yi a yayin neman zabe, shi ne yadda doka ta tsara tafiyar da al’amarin. Marigayi Umar Musa ’Yar’aduwa ne Shugaban kasar Najeriya na farko da ya taba bayyana kadarorinsa ga bainar jama’a cikin wata daya da kama aiki. Shi kuwa mataimakinsa a lokacin, Goodluck Jonathan, abaucewa ya yi ya bi sahun ubangidan nasa. A lokacin da ya zama Shugaban kasa kuwa, an kwashe watanni ana damunsa da batun bayyana kadarorinsa, inda can wani lokaci bayan matsin lamba ya addabe shi, ya fito ya ce ba lallai ne sai ya bayyana kadarorin nasa a bainar jama’a ba, don haka duk mai magana sai dai ya yi ta yi. Kuma lallai ne yin hakan ma na kan tsarin doka.
Ga Shugaba Buhari kuwa, al’amarin ya sha bamban, domin kuwa batun bayyana kaddara a bainar jama’a na daya daga cikin muhimman alkawuran da ya dauka a yayin da yake yakin neman zabe. Don haka abu ne mai matukar muhimmanci gare shi da ya cika wannan alkarai, domin ya faranta wa al’ummar da ke binsa bashin wannan batu. Haka kuma, abu ne mai kyau, ya karfafa wa sauran jami’an da ke cikin gwamnatinsa su yi haka.
Tabbas, mutane sun gama sanin wane ne Buhari kuma sun dade da sanin halinsa na tawali’u da gudun tara abin duniya. Wasu ma tuni suna da masaniyar abin da ya mallaka, wanda kuma ko ya bayyana ba zai wuce haka ba. Tuni wasu suna da hoton gidansa na Kaduna da shanun da ya mallaka a Daura, Jihar Katsina da sauransu. Abin da kawai ake so a fahimtar a nan shi ne, yana da matukar muhimanci ga shugaba ya bayyana kaddarorin nasa, domin kuwa mutane za su fi natsuwa da kara amincewa da al’amarin. Su kuma al’umma ya kamata su kara hakuri, kada su nuna zakuwa kan wannan batu, domin kuwa bai kamata a uzura wa shugaba ya yi abu cikin sauri ba, kamata a yi a bi tsarin da doka ta amince daki-daki.
Abu ne mai matukar muhimmanci ga Shugaban kasa da Mataimakinsa su bayyana kadarorinsu ga al’umma karara. Ta yin haka ne za su samu karsashi da karfin gwiwar umurtar mukarrabansu da su ma su yi haka. Haka kuma yin hakan yana da tasiri wajen bin kadin jami’an da ke yin almundahana da dukiyar al’umma, ta yadda za a magance almundahanar ma gaba daya; musamman ganin cewa yaki da hanci da rashawa da almundahana ne alkiblar wannan gwamnati.
Ya kamata Buhari ya dauki darasi daga gwamnatocin baya, inda suke yin alkawarin bayyana kadarorinsu da shirin yaki da almundahana, amma daga baya sai su juwa baya ga haka da zarar sun dare mulki. A wannan karon ya kamata a ga ‘canjin’ na ainahi da aka yi wa al’umma alkawari.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna