Shugabanci na adalci ke kawo kaunar juna – Sanata Gaya
Mai neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar APC Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya ce shugabanci na adalci ke kawo ci gaban kasa da kaunar juna a tsakanin jama’a. Sanata Kabiru Gaya ya bayyana haka ne a ranar Lahadi lokacin da ya gana da magoya bayansa daga kananan hukumomin jihar 44 a ofishin […]
Mai neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar APC Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya ce shugabanci na adalci ke kawo ci gaban kasa da kaunar juna a tsakanin jama’a.
Sanata Kabiru Gaya ya bayyana haka ne a ranar Lahadi lokacin da ya gana da magoya bayansa daga kananan hukumomin jihar 44 a ofishin yakin neman zavensa da ke Kano.
Sanata Gaya ya ce Allah ne ke bayar da mulki ga wanda Ya so, amma wajibi ne shugabanni su kasance masu adalci da hakuri da mabiya a koyaushe, kuma ta haka ne kadai za a samu zaman lafiya da jagoranci nagari.
Sanata Gaya ya ce ya fito takarar Gwamna ne domin ya kara bada gudunmawarsa ga ci gaban jihar wajen inganta zamantakewar al’umma da kula da lafiya da ilimi da aikin gona da samar da hanyoyin dogaro da kai da bunkasa rayuwar mata da matasa.
Ya ce zai yi amfani da kwarewarsa wajen inganta tattalin arziki da farfado da kasuwanci da aka san Jihar Kano da su. Sai ya yi kira ga al’ummar jihar su sake ba shi dama ya jagorance su domin a cewarsa, yana da kyawawan manufofin kyautata al’amura a jihar da yardar Allah.