Shugabancin Boko Haram: Albarnawi ya ture Shekau
A wannan makon ne wasu rahotanni suka bayyana cewa Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya kara rasa karfi sakamakon yadda Abu Mus’ab ya balle da daruruwan mabiyansa bayan lokaci mai tsawo da bangarorin biyu suka shafe suna takaddama a tsakaninsu, game da shugabancin wasu yankuna a Jihar Borno. Wasu daga cikin mazauna kauyukan da […]

A wannan makon ne wasu rahotanni suka bayyana cewa Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya kara rasa karfi sakamakon yadda Abu Mus’ab ya balle da daruruwan mabiyansa bayan lokaci mai tsawo da bangarorin biyu suka shafe suna takaddama a tsakaninsu, game da shugabancin wasu yankuna a Jihar Borno.
Wasu daga cikin mazauna kauyukan da suka kaurace wa yankunan da Boko Haram din ke da iko, sun bayyana wannan takaddama da ta barke tsakanin Shekau da Albarnawi a matsayin “yakin neman karfin iko.”
Dukkan bangarorin biyu sun ja daga ne bisa habbosar karbe ragamar ba da umarnin kai wasu hare-hare kan rundanar sojin Najeriya da ke yakar kungiyar a wannan yankin. Albarnawi wanda suka fara takun saka da Shekau fiye da shekara guda, da ne ga Shugaban Boko Haram na farko, Muhammad Yusuf, wanda ya kafa kungiyar a shekarun baya.
Rahotannin sun tsegunta wa Aminiya yadda daruruwan sojojin kungiyar suka rasa rayukansu a wannan gwabzawar da ta kaure a tsakanin shugabannin biyu, inda suka bayyana rundunar Abarnawi a matsayin wacce ta yi rinjaye kuma ta fi yawan mabiya.
Wani dan banga mai fafutukar kare al’ummarsa ya bayyana wa Aminiya yadda rashin jituwar ta samo asali tsakanin manyan kwamandojin kungiyar, a lokacin da wani mabiyin kungiyar ya shiga sashen da daya bangaren ke da’awar iko a yankin Dikwa. “Tuni dai aka samu rashin jituwa har ta kai ga ballewar Albarnawi, inda kuma suka rika aiwatar da ayyukan nasu daban-daban amma sun ayyana cewa babu wanda zai shiga yankin da dan uwansa ke da iko. Saba wannan ka’idar ce ta haddasa mummunar gwabzawar da ta yi sanadiyyar rasa daruruwan mabiyan nasu.”
Amma dai rahotannin ba su bayyana yawan wadanda suka rasa rayukan nasu ko suka jikkata ba. Wasu majiyoyin sun kara shaida wa Aminiya cewa wannan arangama ta faru ne a yankunan Gwarimiri da Mulgwailawanti da Golofori da Gaggau da Taye da kuma Chama I da Chama II, inda Albarnawi ya kwace ikon wuraren daga Shekau. Haka kuma wararen da ake ganin Albanawi ya kwace ikon sun hada da Umdarari da Jubul da Shuwari da Fulatar da Shunkori da sauran su. Wuraren galibinsu suna kan iyakokin Gambo-Ngala da Dikwa da Mafa da Konduga da Bama da kuma Gwoza duk a Jihar Borno.