Shugabancin Buhari babbar rahama ce ga kasar nan – Babban Joji
Tsohon Babban Jojin Jihar Kebbi Alhaji Ibrahim Umar ya ce shugabancin Shugaba Muhammadu Buhari babbar rahama bce ga al’ummar Najeriya da kuma Afirka baki xaya.Alhaji Ibrahim Umar ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manem labarai a gidansa da ke Birnin Kebbi, inda ya ce tun daga ranar da Buhari ya ci zabe […]
Tsohon Babban Jojin Jihar Kebbi Alhaji Ibrahim Umar ya ce shugabancin Shugaba Muhammadu Buhari babbar rahama bce ga al’ummar Najeriya da kuma Afirka baki xaya.
Alhaji Ibrahim Umar ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manem labarai a gidansa da ke Birnin Kebbi, inda ya ce tun daga ranar da Buhari ya ci zabe al’amura suka fara canjawa a kasar nan, mutane suka fara samun natsuwa a harkokinsa, sabannin baya da kusan komai ya tabarbare saboda rashin tsaro da ya addabi birni da kauye.
Alhaji Ibrahim Umar ya ce ya kamata mutane su xauki darasi kan halin da suka baro, kowa ya yi kokarin bayar da shawara tagari da goyon baya ga Shugaban kasa, kuma a taya shi da addu’a domin ya samar wa Najereya da cikakken tsaro da bunkasa tattling arziki mai xorewa da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
Alhaji Ibrahim Umar ya ce Shugaba Buhari mutum ne mai girmama doka da oda, don haka wannan wata dama ce da ’yan Najeriya za su yi amfani da ita wajen haxa kai da fahimtar juna su kawar da kabilanci da nuna bambanci don samar da ci gaba ga kasar nan.
“Kowa ya gane cewa shi xan Najeriya kuma ba ya da wata kasa da ta wuce Najeriya, don haka aikin gyaranta na kowa da kowa ne, ba na Shugaban kasa ba ne kaxai, don haka ya zama wajibi mu sani cewa barna ce ake yi rana xaya, amma gyara sai a hankali, domin haka kowa ya bayar da tasa gudunmawa don cimma burinmu na samar da sabuwar Najeriya,” inji shi.
Tsohon Babban Jojin ya ce, ba karamar barna aka yi da dukiyar kasar nan ba kuma ’yan siyasa da wasu ma’aikatan gwamnati a tarayya da jihohi da manyan alkalai da za a binciki abin da suka mallaka sai hankalin jama’a ya tashi saboda suna da hannu dumu-dumu a kan harkar cin hanci da rashawa.
Ya bukaci Shugaba Buhari ya yi gyara a ma’aikatar shari’a ya tantance alkalai na kwarai kada yana gyara wasu na rusawa. Ya ce idan sashin shari’a ya gyaru to ko’ina zai gyaru saboda duk wanda ya yi laifi ko yana neman hakkinsa can yake zuwa, don haka ya zama wajibi a yi garambawul ga ma’aikatan, domin samun cimma burin wannan gwamnati na tsarkake kasa.