Shugabancin INEC: PDP ta nemi a cire Amina Zakari
An bi ka’ida wajen nadinta – Buhari Nadin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Hajiya Amina Zakari a matsayin shugabar riko ta Hukumar Zabe ta kasa a ranar Talatar da ta gabata, bayan cikar wa’adin shugabancin Farfesa Attahiru Jega, ya bar baya da kura, inda Jam’iyyar PDP ta yi zargin an nada ta […]
An bi ka’ida wajen nadinta – Buhari
Nadin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Hajiya Amina Zakari a matsayin shugabar riko ta Hukumar Zabe ta kasa a ranar Talatar da ta gabata, bayan cikar wa’adin shugabancin Farfesa Attahiru Jega, ya bar baya da kura, inda Jam’iyyar PDP ta yi zargin an nada ta a kan mukamin ne don cimma wata boyayyar manufa.
Jam’iyyar PDP ta ce Shugaba Buhari ya nada Amina Zakari ne saboda sanayyar da ke tsakaninsu kuma domin shi da jam’iyyarsa ta APC su yi amfani da ita wajen murkushe PDP a kotunan zabe da kuma zabubbuka masu zuwa musamman zaben gwamnoni a jihohin Kogi da Bayelsa.
Kakakin Jam’iyyar PDP, Mista Olisa Metuh ne ya fadi haka a madadin jam’iyyar, inda ya ce bayan sanayya da ke tsakanin Shugaban kasa Buhari da Amina Zakari akwai Gwamnan wata jiha a Arewa maso Yamma da ya tsaya mata don nada ta a kan wannan mukami.
Ya ce Jam’iyyar PDP ba za ta yarda da nadin nata ba, kuma Shugaban kasa ya gaggauta canja ta.
Sai dai a martanin da Fadar Shugaban kasar ta mayar ga PDP ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ya bi ka’ida wajen nada Amina Zakari a matsayin shugabar hukumar.
A shekaranjiya Laraba ne Jam’iyyar PDP ta zargi Shugaba Buhari kan nada Amina Zakari, inda ta ce ya yi haka ne domin cimma wata boyayyar manufa tasa, don haka ta bukaci a sauke ta daga kan mukamin.
Fadar Shugaban kasar ta ce zargin na PDP ba ya da tushe balle makama.
Wata sanarwa da mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkokin watsa labarai, Femi Adesina ya fitar, ya ce babu kanshin gaskiya a zargin, yana mai bukatar PDP ta kaurace wa zarge-zarge marasa tushe.
Shugaba Buhari ya ce an nada Amina Zakari a kan mukamin ne saboda cancantar da ta yi da kuma muradinsa na ganin an dama da mata a cikin gwamnatinsa.
Gabanin nadinta, Amina Zakari ce mace kadai a cikin kwamishinonin hukumar ta kasa.
Hajiya Amina wadda ta fito daga Jihar Jigawa, ta yi digirinta na farko ne a fannin hada magunguna a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
An nada ta kan mukamin ne bayan saukar Farfesa Attahiru Jega, wanda ya shugabanci hukumar daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2015.
Da farko dai Farfesa Jega ya mika ragamar shugabancin hukumar ne ga Dokta Ahmed Wali a ranar Talata a wani gajeren biki a hedkwatar Hukumar INEC a Abuja, kafin Shugaba Buhari ya nada Amina Zakari riko.
Farfesa Jega ya samu yabo a ciki da wajen kasar nan kan yadda ya gudanar da zaben bana cikin nasara. Kuma saukarsa ta zo ne tare da ta wasu kwamshinonin hukumar shida.
Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya nada Farfesa Jega shugabancin hukumar ne a watan Yunin shekarar 2010, inda ya gaj Farfesa Maurice Iwu, kuma shi ne ya gudanar da zabubbukan shekarar 2011 da 2015. Ya fadi jim kadan da kammala zaben da aka gudanar a ranar 28 ga watan Maris da 11 ga Afrilun bana cewa ba zai nemi a sabunta masa shugabancin hukumar ba. Kuma ya ce idan aka sabunta masa ba zai karba ba.
Farfesa Attahiru Jega shi ne shugaban hukumar zabe da ya gudanar da zabe sau biyu a tarihin Najeriya, kuma ana bayyana zaben 2015 da mafi inganci a tarihin kasar nan.