Shugabancin kasa: Ba ma goyon bayan takarar Gwamna Lamido – PDP

Jam’iyyar PDP, reshen Jihar Jigawa ta nesanta kanta daga kalaman da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar a jihar, Alhaji Aminu Jahun ya yi a jaridu cewa Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido zai tsaya takarar Shugaban kasa kuma jam’iyyar za ta saya masa fom din tsayawa don fuskantar Shugaba Jonathan a zaben share-fage na jam’iyyar.Sakataran Jam’iyyar PDP na […]

Shugabancin kasa: Ba ma goyon bayan takarar Gwamna Lamido – PDP
Shugabancin kasa: Ba ma goyon bayan takarar Gwamna Lamido – PDP

Alhaji Sule Lamido, Gwamnan Jihar JigawaJam’iyyar PDP, reshen Jihar Jigawa ta nesanta kanta daga kalaman da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar a jihar, Alhaji Aminu Jahun ya yi a jaridu cewa Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido zai tsaya takarar Shugaban kasa kuma jam’iyyar za ta saya masa fom din tsayawa don fuskantar Shugaba Jonathan a zaben share-fage na jam’iyyar.
Sakataran Jam’iyyar PDP na Jihar Jigawa, Alhaji Ali Tukur Gantsa ne ya fadi haka a ganawar da ya yi da wakilimmu a ofishin jam’iyyar, inda ya ce maganganun da mataimakin shugaban ya yi na kashin kansa ne ba da yawun Gwamna Lamido ko na jam’iyyar ba.
Alhaji Tukur Gantsa ya ce ba haka ake yin kamfen din siyasa ba, kuma ba a yin bayanai irin haka dole sai shugabannin jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki sun zanta sun samu matsaya kafin su saki baki ga manema labarai.
Ya kuma musanta cewa akwai matsala a tsakanin shugabannin jam’iyyar a jihar, inda ya ce jam’iyyar za ta dauki matakin hukunta Alhaji Aminu Jahun kan kalaman da suka saba wa ka’ida.
A wani labarin kuma dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Roni da Gwiwa da Kazaure da ’Yankwashi, Alhaji Bashir Adamu Jimbo ya bukaci Gwamna Lamido ya amsa kiraye-kirayen da jama’a ke yi masa ya fito takarar Shugaban kasa a zaben badi.
Alhaji Bashir Jambo ya yi wannan kira ne a wajen wani taro da Jam’iyyar PDP reshen Jihar Jigawa ta shirya wa masu ruwa da tsaki a ranar Litinin da ta gabata a dakin karatu na jihar da ke Dutse.
Alhaji Jimbo ya ce muddin Gwamna Lamido ya nuna bukatar tsayawa takarar shugabancin kasar nan a shirye suke su mara masa baya har sai ya kai ga nasara. Game da makasudin taron kuwa cewa ya yi sun tattauna ne a kan abubuwa uku da suka shafi jam’iyyar da ’ya’yanta da kuma makomarta da duba mawuyacin halin rayuwa da talakawan kasar nan suka sami kansu a ciki.
Ya ce kuma sun tattauna batun cike guraben mukaman jam’iyyar da aka rasa sakamakon mutuwar wasu jagororinta da kuma karin girman da wasu suka samu a baya, inda a wannan karo uwar jam’iyyar ta kira taro aka sami ikon cikewa.