Shugabancin kasa: Sulhunta ’yan takarar PDP tana kasa tana dabo

Bisa ga dukkan alamu akwai jan aiki a gaban kwamitin da Kwamitin Amintattun Jam’iyyar PDP ta kasa ta kafa karkashin jagorancin Sanata Walid Jibrin domin fitar da dan takarar Shugaban kasa daya tilo a karkashin jam’iyyar ta hanyar sulhu don tunkarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Jam’iyya APC a zaben badi. A ranar Talatar da […]

Shugabancin kasa: Sulhunta ’yan takarar PDP tana kasa tana dabo
Shugabancin kasa: Sulhunta ’yan takarar PDP tana kasa tana dabo

Bisa ga dukkan alamu akwai jan aiki a gaban kwamitin da Kwamitin Amintattun Jam’iyyar PDP ta kasa ta kafa karkashin jagorancin Sanata Walid Jibrin domin fitar da dan takarar Shugaban kasa daya tilo a karkashin jam’iyyar ta hanyar sulhu don tunkarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Jam’iyya APC a zaben badi.

A ranar Talatar da ta gabata ce Sanata Walid Jibrin ya fitar da wata sanarwa dauke da sakon cewa shi da sauran mambomin Kwamitin Amintattun Jam’iyyar PDP suna kokarin shawo kan masu son tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin jami’iyyar su hada kai, su tattauna sannan su fitar da mutum daya daga cikinsu a matsayin dan takara.

Hakan yana nufin cewa a fitar da dan takarar ba tare da an yi zaben fid-da-gwani da aka saba yi tun dawowar dimokuradiyya a 1999 ba.

A halin da ake ciki dai jadawalin zaben fid-da-gwani na Jam’iyyar PDP ya nuna cewa za a gudanar da zaben fid-da-gwani na dan takarar Shugaban kasa ne a ranar 5 da 6 ga watan Oktoba mai zuwa; kuma tuni kowane daga cikin masu son tsayawa takarar su 12 suka biya Naira miliyan 12 suka karbi fom din tsayawa takarar.

Wadanda suka biya kudin, kuma suka ci gaba da kamfe sun hada da Alhaji Atiku Abubakar da Sanata Ahmed Makarfi da Alhaji Attahiru Bafarawa da Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo na Jihar Gombe da Sanata Jonah Jang da Sanata Rabi’u Kwankwaso da Alhaji Sule Lamido da Dokta Datti Baba-Ahmed da Sanata Dabid Mark da Sanata Bukola Saraki Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato da kuma Alhaji Kabiru Tanimu Turaki.

 A sanarwar da ya fitar, Sanata Walid Jibrin ya ce tuni sun kafa kwamitin da zai tattauna da dukan ’yan takarar domin cimma matsaya.

 “Mun umarci mambobin kwamitin su tattauna da dukan ’yan takarar domin a samu maslaha; muna so su zakulo mana dan takarar guda daya tilo domin mu fuskanci zabe mai zuwa da karfinmu,” inji shi. 

Ya kara da cewa: “Mun dauki wannan mataki ne domin kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu ta PDP ya ba mu karfin tsara doka da oda ga mambobin jam’iyyar domin kaiwa ga nasara. Idan mambobin kwamitin da muka nada suka kammala ayyukan da muka ba su, mu kuma za mu tattara mu mika wa Babban Kwamitin Gudanarwar Jam’iyya (NWC.”

To sai dai kuma bisa ga dukan alamu wanki hula zai kai su Sanata Walid Jibrin dare, musamman idan aka yi la’akari da furucin da ke fitowa daga wadansu daga cikin ’yan takarar.

Misali Alhaji Atiku Abubakar, wanda bisa ga dukan alamu yana so sauran ’yan takarar 11 su daga masa kafa, ya yi wani furuci a lokacin da ya kai ziyara babban offishin Jam’iyyar PDP na Jihar Jigawa, inda ya ce yana rokon tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido ya daga masa kafa. “Ina fatar kanena Sule Lamido ya janye takarar da yake yi kuma ya mara mini baya,” inji shi.

 “Ina ganin na cancanci in samu goyon bayansa a matasayinsa na kanena, domin hasali ma iyayena daga Jihar Jigawa suke. Ina so ya yi abin da marigayi Shugaban kasa Umaru ’Yar’aduwa ya yi, lokacin da ya janye daga takarar Gwawna a Jihar Katsina domin ya mara wa yayansa Shehu Musa ’Yar’aduwa wanda ke neman Shugaban kasa,” inji Atiku.

 To sai dai bisa ga dukan alamu bayani wya sosa wa Alhaji Sule Lamido rai.

Wakilinmu ya tuntubi tsohon Gwamnan kuma ga abin da ya ce. “Hakika Atiku ya je Jihar Jigawa kuma ya yi wannan bayani a ofishin Jam’iyyar PDP amma ba na wajen.Ni dai na san ya ziyarce ni a gidana da ke Bamaina kuma mun tattauna al’amuran siyasa amma ba mu yi maganar in janye masa ba.”

 “Tabbas ya grime ni a shekaru amma ni kuma na girme shi a fagen siyasa, don haka ina ganin shi ne ya dace ya janye kudirinsa ya mara mini baya domin in zama Shugaban kasa. Ina so ka gane cewa ni ina Majalisar Wakilai a lokacin da shi Atiku yake aikin Kwastam, don haka ai ni ne gaba da shi a fagen siyasa. Ni ba zan janye wa kowa ba domin ina da magoya baya wadanda sun amince da ni kuma suna tare da ni,” inji shi.

 Shima tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Ahmad Makarfi, ya shaida wa wakili mu ta hanyar sakon waya cewa maganar sulhu a bai wa mutum daya takara ba ta taso ba.

“Ina wajen taron Kwamitin Amintattun Jam’iyya kuma zan iya tuna cewa abin da aka tattauna shi ne an kafa kwamitin da zai kokarta ya rage yawan ’yan takara. An shaida wa kwamitin cewa ya yi kokarin rage ’yan takarar ba tare da ya tilasta wa kowa ba. Haka kuma an ce kwamitin ya yi kokarin rage kaifin adawa idan har dukan ’yan takarar suka ce ba za su janye ba,” inji shi.

“Don haka ni a ganina ba maganar fitar da dan takara daya aka yi ba, an tattauna ne kan yadda za a fid-da-gwani bisa adalci,” inji shi.

 Shi ma Sanata Datti Baba Ahmed ya shaida wa wakilinmu ta hanyar WhatsApp cewa “Ba zan ari bakin Kwamitin Dattawa in ci musu albasa ba, amma a ganina suna kokarin kawo sulhu ne a tsakanin ’yan takara. Don haka ni a matsayinna na dan takara, ina so in shaida maka cewa lallai ina nan a kan bakana, kuma ina fatar sauran ’yan takarar su janye mini saboda wasu dalilai.”

“Ni fa ina ganin zai yi matukar wuya in janye wa wani dan takara saboda ni ne alkiblar matasa, duniya ta canja yanzu matasa ne ke mulki. Bayan haka ina da wasu alamomi masu yawa da ke nuna cewa ni ne kadai zan kayar da Buhari,” inji shi.

 Shi ma Sanata Bukola Saraki ya ce kowa ya baje kolinsa kawai. Ya ce maganar janye wa wani ba ta taso ba, domin ita Jam’iyyar PDP ba kamar Jam’iyyar APC ba ce.

 “Ai maganar a janye wa wani ba ta taso ba. Muna so a yi zaben fid-da-gwani kuma kowa ya iya ruwa sai ya fid da kansa,” inji shi.

 Kusan bakinsa ya zo daya da na Sanata Kwankwaso, wanda ya yi bayani a Jihar Neja a ranar Laraba inda ya ce lallai yana nan daram a kan bakarsa ta neman Shugaban kasa.

 Bisa ga dukan alamu dai zai yi wuya a shawo kan ’yan takarar PDP su yarda su fitar da mutum daya daga cikinsu, domin kusan kowannensu yana ganin shi ne ya fi dacewa. 

Masana al’amuran siyasa dai suna ganin a karshe dai dole ne a gudanar da zaben fid-da- gwani a PDP, wanda hakan ka iya wargaza jam’iyyyar idan har wadansu daga cikin masu son tsayawa takarar suka fahimci cewa an yi musu ba daidai ba.

 Gwamnonin jam’iyyar a karkashin Gwamna Ayo Fayose mai barin gado sun ce za su tsoma baki su ga ko za a iya yin sulhu a tsayar da mutum daya. Sai dai masana suna ganin wannan batu maganar ba mai yiwuwa ba ce domin tun farko Gwamna Fayose tare Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike, su ne kanwa uwar-gami, domin su ne suka saka yawancin masu son tsayawa takarar suka fito bayan sun yi alkawarin mara musu baya.