Shugabancin kasa: Yanzu lokacin Arewa ta Tsakiya ne – Saraki
Shugaban Majalisar Dattawa, kuma mai neman tsayawa takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP, Sanata Bukola Saraki ya ce idan aka zabe shi a matsayin Shugaban kasa a zaben badi, zai gudanar da mulki na adalci ga duk shiyyoyin kasar nan shida. Saraki ya bayyana haka ne a Jos lokacin da ya gana da wakilan Jam’iyyar […]

Shugaban Majalisar Dattawa, kuma mai neman tsayawa takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP, Sanata Bukola Saraki ya ce idan aka zabe shi a matsayin Shugaban kasa a zaben badi, zai gudanar da mulki na adalci ga duk shiyyoyin kasar nan shida.
Saraki ya bayyana haka ne a Jos lokacin da ya gana da wakilan Jam’iyyar PDP na jihar a sakatariyar jam’iyyar.
Saraki wanda tsohon Gwamman Jihar Kwara ne ya bayyana cewa lokaci ne da yankinsa na Arewa ta Tsakiya da ya hada jihohin Kwara da Filato da Benuwai da Neja da Kogi da Nasarawa ya kamata ya samar da Shugaban kasa.
Ya ce, “Yanzu lokacinmu ne, wato yankin Arewa ta Tsakiya don mu samar da Shugaban kasa a yankinmu na Arewa ta Tsakiya muna bukatar mutum mai jajircewa da zai yi yaki don talakawa, ana bukatar mutum mara tsoro kamar ni.”
Saraki wanda kuma tsohon Shugaban kungiyar Gwamnoni ta Najeriya ce ya ce, mutanen jihohin shiyyar duk al’umma daya ce, don haka duk wanda ya samu mulki daga yankin to daya ne.
Ya ce, “Yankin Arewa ta Tsakiya ya jajirce wajen samar da Najeriya a matsayin kasa daya, ba ma nuna bambanci, amma a zahirin gaskiya ba a taba samun rarrabuwar kai a kasar nan kamar wannan lokaci ba.”
Ya ce, idan ya samu mulki zai rungumi kowane yanki, “Zan samar da gwamnatin da kowa zai samu ta-cewa, zan samar da kasar da kowa zai yi alfahari da kasancewar dan kasar, zan kuma zama Shugaban kasar da mutanen kasar nan za su yi alfahari da ni,” inji shi.
Ya ce idan har aka zabe shi Shugaban kasa to ba zai nuna wariya ko fifita wani yanki ko yare ba.
“Idan na zama Shugaban kasa zan kai gwauro in kai mari don kare rayuwarku, zan tabbatar an hukunta duk wanda aka samu da laifi, ni Bukola zan tsaya don yi muku yaki, zan samar da kasar da za ku yi alfahari da ita,” inji shi.