Shugabancin majalisa: Yadda PDP ta yi wa APC wala-wala

Ga dukkan alamu babbar jam’iyyar adawa wato PDP ta shammaci Jam’iyyar APC mai mulki inda ta yi mata wala-wala wajen dora mata shugabannin majalisar dokoki ta kasa da ba su APC ta so su kasance shugabannin ba a ranar Talatar da ta gabata, inda Sanata Bukola Saraki na sabuwar PDP (daga Jihar Kwara) da ya […]

Shugabancin majalisa: Yadda PDP ta yi wa APC wala-wala
Shugabancin majalisa: Yadda PDP ta yi wa APC wala-wala

Ga dukkan alamu babbar jam’iyyar adawa wato PDP ta shammaci Jam’iyyar APC mai mulki inda ta yi mata wala-wala wajen dora mata shugabannin majalisar dokoki ta kasa da ba su APC ta so su kasance shugabannin ba a ranar Talatar da ta gabata, inda Sanata Bukola Saraki na sabuwar PDP (daga Jihar Kwara) da ya koma APC da Yakubu Dogara shi ma na sabuwar PDP (daga Jihar Bauchi) da ya koma APC suka lashe zaben Shugaban Majalisar Dattawa da ta Wakilai.

An dauki tsawon makonni ana muhawara da kamun kafa da zame kafa da munafunce-munafunce na siyasa, kan wadanda za su shugabanci sabuwar majalisar dokokin ta kasar nan, inda aka samu wasu kungiyoyi a tsakanin zababbun sanatoci da ’yan majalisar wakilai masu suna Unity Forum da Like Minds Group da suke goyon bayan Lawan da Saraki, kafin Jam’iyyar PDP ta yi wa APC juyin mulkin da ya jawo Sanata Abubakar Bukola Saraki da ya bijire wa umarnin jam’iyyarsa ta APC ya fito takarar kujerar Shugaban Majalisar Dattawa da APC ta zabi Sanata Ahmed Lawan a zaben gwajin da ta gudanar a makon jiya, inda a karshe Sanata Saraki ya zama shugaban majalisar a daidai lokacin da sanatocin jam’iyyarsa na APC ke jiran ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda aka sa ran ya kawo maslaha kan batun.
Matsalar hadaka a tsakanin tsofaffin jam’iyyun ACN da ANPP da CPC da New PDP ta taka rawa wajen bijire wa Jam’iyyar APC a zaben shugabannin majalisar, sakamakon yadda sauran abokan hadakar suka lura za su tashi a tutar babu a sabuwar gwamnatin da aka kafa. Jam’iyyar CPC dai ta samu Shugaban kasa, sai ACN Mataimakin Shugaban kasa, yayin da ANPP za ta samu shugaban Majalisar Dattawa, sai ACN ta sake samun shugaban Majalisar Wakilai, ita kuma New PDP ta tashi a tutar babu idan aka bi tsarin na APC.
Ana jin wannan ne ya sa Sanata Saraki da wasu sanatocin APC bakwai da galibinsu na New PDP ne suka hade kai da sanatocin Jam’iyyar PDP 49 suka yi wa APC shigar sauri suka tsira da kujerar Shugaban Majalisar Dattawa da ta Wakilai, inda suka yi zaman zaben shugabannin majalisar a daidai lokacin da Sanata Lawan da sauran sanatocin APC 50 ba su nan.
Wannan wala-wala ta PDP ta jawo wa APC rasa mukamin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan inda tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Sanata Ike Ekweremadu na Jam’iyyar PDP ya sake komawa kan kujerarsa.
A daidai lokacin da magoya bayan Sanata Lawan suka hallara a Cibiyar Taro ta Duniya (ICC) da ke Abuja don ganawa da Shugaba Buhari da kuma shugabannin jam’iyyarsu ta APC ne sanatoci 57 suka yi saurin zuwa zauren Majalisar Dattawan domin kaddamar da sabuwar majalisar. A can cibiyar taro ta ICC ne kwatsam, sai sanatocin APC suka ga an fara zaman majalisar ta akwatin talabijin a lokacin da suke jiran isowar Shugaban kasar, nan suka fito babu shiri, sai dai kafin su isa zauren majalisar, magoya bayan Saraki sun bayyana shi a matsayin dan takara daya tilo.
Akwai bayanan da suke cewa, cikin wadanda suka shirya wannan wala-wala har da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da wasu tsofaffin gwamnonin PDP da suka koma APC da suka hada da tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko,wadanda dukkansu, ’yan New PDP ne da suka shiga hadakar, sai tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Ahmed Sani Yarima da tsohon Gwamnan Jihar Gombe Sanata danjuma Goje na New PDP da tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio da tsohon Gwamnan Jihar Abiya, Theoodore Orji da kuma tsohon Shugaban Majalisar Tarayya kuma Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da Gwamnan Jihar Ekiti Cif Ayo Fayose da Gwamnan Jihar Ondo Dokta Segun Mimiko da kuma Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike.
Baya ga batun mayar da bangaren New PDP gefe da ake zargin jagoran APC Bola Tinubu da yi akwai kuma zargin cewa tsofaffin gwamnonin da suka samu shiga Majalisar Dattawa suna tsoron Shugaba Buhari zai iya nuna halin ba-sani-ba-sabo ga duk wani tsohon Gwamna da ke da kashi a gindi. Wata majiya ta ce wannan ne ya sa ire-iren wadannan tsofaffin gwamnoni suka gudanar da wani taro a otel din NICON Hilton da ke Abuja a makon jiya, inda suka tattauna a karshe suka yanke shawarar goya wa Saraki baya don ya shugabanci Majalisar Dattawa ta yadda zai kare su koda Shugaban Buhari zai waiwayi tsofaffin gwamnonin da suke da kashi a gindi.
An ruwaito cewa Buhari ya shaida wa ’yan majalisar ba ya da dan takara, amma ya shaida wa shugabannin Jam’iyyar APC da ’yan majalisar su tabbatar ba su zaba masa mutumin da ake tuhuma kan kowace badakala ba. Wannan ne ake jin dalilin da ya sa APC ta zabi Sanata Ahmed Lawan daga Yobe don shugabancin Majalisar Dattawa sai Mista Femi Gbajabiamila don takarar shugabancin Majalisar Wakilai.
Wata majiya da ke kusa da majalisar ta shaida wa wata kafar labarai cewa: “Galibin wadannan mutane (gwamnoni) suna da kashi a gindi kan yadda suka tafiyar da mulkin jihohinsu.” Don haka suka gwammace su juya wa jam’iyyarsu baya domin samun wanda zai taimaka wajen rufa musu asiri.
A wajen taron mahalartarsa sun ce Sanata Lawan na kusa ne sosai da Shugaba Buhari. Lawan shi ne ko’odinetan kamfe din Buhari a zaben Shugaban kasa na shekarar 2007 a Jihar Yobe, lokacin da ya yi takara a karkashin tsohuwar Jam’iyyar ANPP.
Duk da cewa bayanai sun nuna cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Dabid Mark ya fi karkata ga goyon bayan Sanata Ahmed Lawan ya gaje shi, wata yarjejeniya da aka kulla a gidansa bayan kai-kawo da shige-shige a ranar Lahadin da ta gabata zuwa wayewar Litinin a tsakanin bangaren Saraki da Jam’iyyar PDP ne ta haifar da matsayar sanatocin PDP su mara wa Saraki da Dogara duk da cewa suna daga cikin wadanda suka yi wa PDP tawaye a karshe ta fadi a zaben da ya gabata.
Wani abin da ake ganin ya taimaka wajen samun wannan baraka shi ne yadda wasu shugabannin APC suke jin haushin yadda Shugaba Buhari yake fifita Uban Jam’iyyar APC Ahmed Bola Tinubu tare da mayar da shi tamkar shi ne kadai jagoran kawo canji a kasar nan. Wasu kuma na ganin Shugaba Buhari ya ba Tinubu karfin mai yawa don haka akwai bukatar ya rage yadda yake ba shi iko haka.
Sannan Jam’iyyar APC ta gaza fitar da tsarin raba mukamai a majalisar dokokin wanda akwai bukatar a samu haka don samar da hadin kai. Masu wannan ra’ayi na ganin da APC ta yi haka ba za a samu kaiwa ga halin da ake ciki a yanzu ba. Kuma wannan gazawa ce ta ba bangaren Saraki damar sake fasalin siyasar kasar nan ta hanyar jawo Sanata Ekweremadu daga Kudu maso Gabas ya zama mataimakinsa mukamin da in da an bi ta Jam’iyyar APC yankin ba zai samu ba.
Jam’iyyar APC har wa yau ta manta da matsayin Saraki a siyasa, wanda bayan ya gaje ta daga mahaifinsa Sanata Sola Saraki, shi kansa ya shugabancin Majalisar Gwamnonin Najeriya, kuma ya taka rawa a zamanin gwamnatin marigayi Shugaba Umaru ’Yar’aduwa lamarin da ya sa yake da karfin fada-a-ji da magoya baya da abokan siyasa a sassan kasar nan.
Har wa yau shi kansa Shugaba Buhari bai taimaka wa jam’iyyar tasa ba, inda ya nuna cewa ba ya da dan takara kuma duk wanda ’yan majalisun biyu suka zaba zai yi aiki da su, sannan ya sanya kafa ya fice zuwa taron G7 a kasar Jamus ba tare da ya tattauna da sanatocin ba, kuma da ya dawo bai hanzarta kiransu gaba daya don ganawa da su ba, har lokaci ya kure, lokacin da Jam’iyyar PDP ta riga ta bayyana cewa magoya bayanta su zabi Saraki da Dogara a zaben shugabancin kujerun biyu.
Sai dai duk da cewa Shugaba Buhari ya ce zai yi aiki da sababbin shugabannin biyu, rashin amincewar Jam’iyyar APC da kuma bangaren Sanata Lawan tambayar da ake yi ita ce ko Saraki zai ci gaba da shugabancin majalisar ba tare da matsala ba, ko kuwa za a maimaita abin da ya faru a 1999, lokacin da marigayi Sanata Ebans Enwerem ya zama shugaban majalisar bisa goyon bayan Shugaba Obasanjo,ta hanyar samun goyon bayan mambobin tsohuwar Jam’iyyar AD inda ya kada marigayi Sanata Chuba Okadigbo wanda shi ne dan takarar da PDP take so.
Atiku wanda suka fito daga iyalan siyasar marigayi Shehu ’Yar’aduwa sun goya wa Okadigbo baya ne, kuma Enwerem bai fi wata shida ba aka tsige shi aka maye gurbinsa da Okadigbo, tun daga nan aka shiga gwagwarmaya kan kujerar a tsakanin sanatocin Kudu maso Gabas.
A bangaren Majalisar Wakilai lamarin bai yi zafi da munin na Majalisar Dattawa ba, inda kusan daukacin wakilan majalisar ne suka kada kuri’a a zaben da y aba Dogara nasara a kan Gbajabiamila wanda APC ta tsayar takarar kujerar. Zaben dai ya yi zafi inda Dogara ya samu kuri’a 183 Gbajabiamila ya samu 174.
Sai dai a yayin da ake zargin Shugaba Buhari da kin zuwa ganawa da sanatocin APC, Kakinsa Garba Shehu ya ce Shugaba ba ya ki zuwa ba ne da gangan, bai je ba ne saboda ya samu labarin Saraki da bangarensa sun riga sun zabi shugabannin majalisar. Garba Shehu ya ce Buhari ya bukaci Akawun Majalisar da ya dan jinkirta lokacin zaben da wata majiya ta ce zuwa karfe 11:00 na safe, amma Akawun Majalisar da Bukola Saraki suka ki aiki da bukatar Shugaban wanda ya dawo cikin dare daga kasar Jamus daga taron G7.
Buhari dai ya ce duk da haka zai yi aiki da ko wa ke shugabancin Majalisar Dattawan, amma zai goyi bayan duk wani mataki da Jam’iyyar APC za ta dauka a kai. Kuma ya tabbatar cewa Shugaba Buhari bai aike da sakon taya murna ga Bukola Saraki da Yakubu Dogara kan nasararsu a zaben ba.
Wasu sanatoci sun zargi Akawun Majalisar Salisu Maikasuwa da hada baki da sanatocin PDP don yi wa APC zagon kasa. Sanata Barnabas Gemade wanda ke cikin masu wannan ra’ayi ya ce tunda an sanar da akawun batun taron sanatocin APC bai kamata ya bude majalisar ba, sai ya tabbatar sanatocin sun hallara gaba daya, amma bai yi haka ba, sai ya bude majalisar kuma ya jagorancin gudanar da zaman majalisar tare da zaben shugabanninta ba tare da an cika ka’idar mambobin da suka kamata su yi zabe ba. Don haka ya ce za su garzaya kotu don warware wannan zabe da aka yi wa Saraki wanda ya ce bai samun kashi biyu bisa uku da doka ta tanada ba kafin a gudanar da shi.
Sai dai a martanin da Kakakin Jam’iyyar PDP na kasa Olisa Metuh ya mayar kan dambarwar ya ce sakacin Jam’iyyar APC ne ya jawo mata wannan matsala. Ya ce babu ruwan PDP a takaddamar da ta shafi APC, ita ta kasa kintsa gidanta, kuma ’ya’yanta ne suka yi mata tawaye kafin PDP ta ce a goyi bayan wasu daga cikin ’yan takarar shugabancin majalisun biyu.