Shugabancin Najeriya na da wahala – Babangida
Tsohon Shugaban Kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya ce shugabancin Najeriya abu ne mai wahala. Janar Babangida ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai sarkakiya da wahalar gudanar saboda mabambanta jama’arta da kuma irin mutanen da take da su. A cewarsa bambance-bambancen a kullym suna bayar da damar suka da muhawar ne bisa bambancin […]
Tsohon Shugaban Kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya ce shugabancin Najeriya abu ne mai wahala.
Janar Babangida ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai sarkakiya da wahalar gudanar saboda mabambanta jama’arta da kuma irin mutanen da take da su. A cewarsa bambance-bambancen a kullym suna bayar da damar suka da muhawar ne bisa bambancin yankuna wadanda a wasu lokuta suke jawo tayar da jijiyar wuya da kuma zaune-tsaye. Janar Babangida ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata, lokacin da ayarin shugabannin marasa rinjaye na Majalisar Wakilai a karkashin jagorancin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Mista Ndudi Elumelu suka kai masa ziyarar ban-girma a gidansa da ke Minna a Jihar Neja. Duk da haka ya bayyana Najeriya da cewa kasa ce mai tarin albarka da kuma ababen burgewa. Ya yi kira ga shugabannin siyasa da kada su yarda wadannan bambance-bambance su firgita su, maimakon haka su mayar da hankali wajen daidaita wadannan bambance-bambance ta yadda za a ci gajiyarsu. Ya ce wadanda suka amso mulkin kasar nan sun yi aiki wurjanjan wajen kafa kakkarfan harsashi ga kasar nan duk da dimbin matsalolin da suka gada. Ya ce wakilan Majalisar Dokoki ta Kasa kada su bari a rusa kyawawan ayyukan da magabata suka assasa kasar nan a kai na hadin kai. “Ina lura da yadda al’amura suke tafiya a wannan kasa, kuma ina da sha’awata sosai kan yadda abubuwa suke a halin yanzu, kuma ina ganin shugabannin Majalisar Wakilai da shi Shugaban Majalisar da ’yan adawa da dukkan jama’a, suna bakin kokarinsu. Kuna wakiltar jama’a kuma abin da jama’ar suke nema ke nan, don haka ina yaba muku a kan wannan namijin aikin da kuke yi, kada ku karaya,” inji shi.
Tsohon Shugaban ya ce bayan kammala zaben shugabannin majalisa, yanzu abin da ya rataya a wuyansu shi ne aiwatar da dokokin da za su kawo ci gaba mai ma’ana ga al’ummar kasa.
A jawabin Elumelu, ya ce sun zo Minna ne domin gabatar da kansu a shugabannin matsayin marasa rinjaye a majalisar, kuma su gode masa a kan rawar da ya taka wajen samun nasararsu, sai ya yi addu’ar Allah Ya bai wa tsohon Shugaban Kasar lafiya.