Shugabancin PDP: Dokpesi ya goyi bayan Bode George

Tsohon shugaban Hukumar Kula da tashoshin jiragen ruwa (NPA), wanda ke fafutukar neman zama shugaban Jam’iyyar PDP a zaben da za a yi a babban taron jam’iyyar mai zuwa, Cif Olabode George ya ce zai zama shugaba na kowa idan har ya samu nasara. Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar, ya yi wannan jawabin ne a Abuja […]

Shugabancin PDP: Dokpesi ya goyi bayan Bode George

Tsohon shugaban Hukumar Kula da tashoshin jiragen ruwa (NPA), wanda ke fafutukar neman zama shugaban Jam’iyyar PDP a zaben da za a yi a babban taron jam’iyyar mai zuwa, Cif Olabode George ya ce zai zama shugaba na kowa idan har ya samu nasara. Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar, ya yi wannan jawabin ne a Abuja a lokacin da yake bude ofishin yakin neman zabensa.

“Zan zama shugaba na kowa. Zabe za mu yi, kuma duk wanda ya samu nasara a zaben, za mu ba shi goyon baya dari-bisa-dari idan har anyi zabe mai nagarta.

“Idan Allah Ya sa na zama shugaban wannan jam’iyyar, zan yi aiki da kowa ba tare da nuna bambanci ba, zan yi iya kokarina. 

“Muna bukatar shugaba wanda ya san ka’idodin tafiyar da wannan jam’iyyar,” inji Bode. Da yake jawabi a kan Jam’iyyar APC mai mulki a yanzu, cewa ya yi “Kuna ganin yadda ‘yan APC suka lashe zabe, amma kansu ba hade yake ba. Ba su da ko kwamitin amintattu,” inji shi.

Babban abin mamaki a wajen taron bude ofishin, shi ne yadda Cif Raymond Dokpesi ya halarci taron, duk da cewa shi ma yana cikin masu neman shugabancin jam’iyyar. A cewarsa “Ina godiya ga Bode George musamman bisa yadda ya ba Jam’iyyar PDP gudunmuwa, da kuma gudunmuwar da ya ba Najeriya baki daya.

“Na halarci wannan taron ne domin in nuna goyon baya ga Bode George domin na san zai iya jagorantar wannan jam’iyyar.

“Mun yi taro na musamman, inda muka amince cewa wannan zaben da za a yi na cikin gida ne, duk wanda ya samu nasara za mu ba shi goyon baya. Ba za mu samu nasara a zaben 2019 ba idan har babu irin su Bode George,” inji Dokpesi.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon Ministan Ayyuka, Sanata Adeseye Ogunlewe, tsohon Ministan Harkokin ‘yan Sanda, Alhaji Adamu Maina Waziri da sauransu.