Shugabancin PDP:Wasu gwamnoni na yunkurin nada Secondus

Yayin da babban taron jam’iyyar PDP ke kara karatowa ana zargin wasu gwamnonin jam’iyyar  da yunkurin nada Yarima Uche Secondus a matsayin shugaban jam’iyyar. Secondus ya taba zama mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa zamanin Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu daga bisani ya zama mukaddashin shugaban jam’iyyar lokacin da rikici ya mamaye maigidansa a ranar 20 ga […]

Shugabancin PDP:Wasu gwamnoni na yunkurin nada Secondus

Yayin da babban taron jam’iyyar PDP ke kara karatowa ana zargin wasu gwamnonin jam’iyyar  da yunkurin nada Yarima Uche Secondus a matsayin shugaban jam’iyyar.
Secondus ya taba zama mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa zamanin Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu daga bisani ya zama mukaddashin shugaban jam’iyyar lokacin da rikici ya mamaye maigidansa a ranar 20 ga watan Mayun shekarar 2015.
A zamaninsa, Secondus wanda ake zaton zai sauka bayan ’yan watannin, ya makale a kujerar shugaban jam’iyyar har sai da Barista Ahmed Gulak, tsohon mai baiwa shugaba Goddluck Jonathan shawara ya kai shi kotu.
Wata majiya da ke kusa da jam’iyyar  ta nuna cewa wasu membobin kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar da wasu jigajigan jam’iyyar sun rabu kan goyon bayan da gwamnonin ke yi wa Secondus amma jam’iyyar na yi wa lamarin taka-tsantsan don kaucewa rikici.