Shugabanin APC na Gombe duk ’yan PDP ne – Adamu Abubakar
Wani matashin dan siyasa kuma jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Gombe Alhaji Ahmad Adamu Abubakar, ya nuna rashin gamsuwars ’ya’yan APC na jihar kan shugabannin rikon da aka nada wa jam’iyyar.Ahmad Adamu Abubakar, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kira taron manema labarai a Gombe inda ya ce ’ya’yan APC na Gombe […]

Wani matashin dan siyasa kuma jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Gombe Alhaji Ahmad Adamu Abubakar, ya nuna rashin gamsuwars ’ya’yan APC na jihar kan shugabannin rikon da aka nada wa jam’iyyar.
Ahmad Adamu Abubakar, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kira taron manema labarai a Gombe inda ya ce ’ya’yan APC na Gombe ba su gamsu da mika jagorancin jam’iyyar ga Barista Magaji Doho ba, domin dan PDP ne ba dan ANPP ko CPC ko ACN ba kuma bai taba zama dan jam’iyyar adawa ba.
Ya ce su ne suke rike da Jam’iyyar APC tunda aka yi mata rijista har zuwa hade ta a APC don haka su ya kamata su fitar da wanda zai shugabanci jam’iyyar ba kawai su wayi gari an dora musu dan PDP ba.
A cewarsa Magaji Doho da aka turo ya zama shugaban riko da sauran shugabanin da aka nada duk ’yan PDP ne, kuma Jam’iyyar PDP ba ta cikin jam’iyyun da suka yi hadaka don haka ba su cancanci shugabancin APC ba.
Ya ce, tsohon Gwamnan Jihar Sanata danjuma Goje da ya shiga APC muna mutunta shi amma sai ga shi bai yi mana daidai ba, inda ya kawo mana shugabanin daga PDP mu ’yan asalin APC an bar mu ba komai.
Ya ce sun dau matakin rubuta kokensu zuwa ga uwar jam’iyyar ta kasa idan kuma ba ta yi komai ba za su bude ofis din da ’ya’yan jam’iyyar zalla za su shugabance ta ba ’yan PDP ba.