Shugabanni Nagari!
Akwai abubuwa da dama da ke sa wadansu mutane su karbu a tsakanin al’umma, ma’ana su kasance masu jan ragamar jama’a ko kuma masu fadar abu nan da nan jama’a, wasu ma ba tambaya, su bi, ko su aikata abin da aka bukace su. Daga cikin wadannan abubuwa, akwai so da kauna da mutane ke […]
Akwai abubuwa da dama da ke sa wadansu mutane su karbu a tsakanin al’umma, ma’ana su kasance masu jan ragamar jama’a ko kuma masu fadar abu nan da nan jama’a, wasu ma ba tambaya, su bi, ko su aikata abin da aka bukace su. Daga cikin wadannan abubuwa, akwai so da kauna da mutane ke yi wa irin wadannan mutane, ba kuma don komi ba sai don sun kasance gwarzayensu, mutanen da suke ganin ba su taba cutar su, in kuma sun ba su amana, ba za su ci a kowane irin hali ba. Irin wa]annan mutane za ka taras cewa an taba gwada su, kuma an ga cewa ba su ba da kunya ba. Saboda haka duk lokacin da wani abu ya taso, na sa wasu a gaba, su ne za ka ga an tura gaban, domin su yi wa jama’a limanci.
Akwai kuma wadanda jama’a ke “so da kauna”, ba don Allah ba, ko dai shugabanni ne suka ]ora su bisa shugabanci da karfi da yaji ko su suka haye, don haka ba sa neman yarda da amincin jama’ar tasu. Haka za su kasance a gaba, abin da suka fa]a, jazaman, mai kyau ko marar kyau, idan an biya masu bukatunsu, shi ke nan.
Akwai kuma wadanda ake bi sau da kafa ba don komi ba sai don addini ya ba su wannan tsarin na shugabanci, shi ne kuma ya yi masu tanadin matsayin da za su kasance a bisa. A bisa irin wannan tsari da wuya ake ja-in-ja da wanda Allah ya ba wannan matsayi ko shugabanci, domin fa]ar shugaban ba tasa ba ce, ta Maiduka ce, kenan ja da wannan shugaba, tamkar ja da Allah ne.
Akwai kuma wadanda ake bi sau da kafa, domin sun gaji matsayin ne, ba kuma wani da yake da ikon ya ce da su ba haka ba. Su ne za su sa }afa su shure, su sa a daure ko a kashe, babu mai cewa uffan, domin sun sami wannan matsayi ne daga ruhin gidan da ya samar da su.
Akwai mutane daban-daban a duniya da suke samun matsayi da mukami bisa mabamnbanta dalilai, su kuma talakawa na dubar su ne bisa irin wannan matsayi da suka samu kansu ko aka ba su ko kuma suka gada ko suka gina wa kansu domin yanayin rayuwarsu ta yau da kullum.
An yi irin wa]annan mutane a kowane sashe na duniya, za a iya tunawa da Malcom d a Amurka, wanda ya ginu a zukatan jama’ar kasar Amurka, ba don komi ba sai don kishin talaka da kuma bakar fatar Amurka a zamanin mulkin wariya. Za a iya tunawa da Adolf Hitler, wanda ya mulki kasar Jamus da mugun hannu, ya sanya Yahudawa sama da miliyan 6 suka tunkushi birji, saboda mulkin kama-karya, amma har ta Allah ta kasance an dauka jama’ar kasarsa suna son sa da kaunarsa saboda tsoro da gaba da ya assasa a zukatansu. Za a iya tunawa da Mahatma Gandhi, na Indiya, wanda saboda saukin kansa da juriyar wahala da kuma nema wa talaka ’yanci ya kasance tamkar wani annabi-annabi a tsakanin Indiyawa. Haka kuma ba za a manta da Rebaran Martin Luther King na Amurka ba, wanda daga cikin Coci ya canza rayuwar Amurkawa da tsarin mulkin Amurka, wanda da wuya a samu irin sa a Amurka, cikin karnoni masu zuwa. Haka kuma za a iya tunawa da Sarkin Sarakuna, Haile Salasie na Habasha da Sarkin Sarakuna Bokassa na kasar Afirka ta Tsakiya, wanda maganarsu tamkar wahayi ce ga mutanen kasarsu, ba wai don suna son su ba, sai dai don gudun bacin rana, kurum.
Kusan dukkan wadannan mutane da irin turbar da suka biyo domin kai wa ga wannan matsayi nasu, wasu kamar yadda na bayyana, saboda kaunar zuci ce jama’a suka so su, wasu saboda tausasawa, wasu saboda sun tashi sun ga ana mulkinsu ne kurum, ba su da ta cewa, wasu kuma sun bi wannan mataki ne ba don komi ba sai don shi ne suke ganin cewa zai kasance mai fitar da su da kuma al’ummarsu daga cikin halin da suke ciki.
To sai dai idan aka yi la’akari da irin rayuwar wa]annan mutane da yadda suka kare da kuma tarihin da suka bari a doron kasa, za a fahimci cewa, wasu sun yi nakasu ne, wasu kuma sun yi abin a zo a gani. Duk da irin mulkin Hitler da yadda ya kasance kamar wani dodo a Turai, ba abin da ake iya tunawa da shi a halin yanzu irin yadda ya kashe mutane ba ji, ba gani, ya kuma jawo yakin duniya. Shi kuwa Mahatma Gandhi, tarihinsa a tsakanin talakawa bai wuce wanda ya samar da sabuwar kasar Indiya cikin ruwan sanyi ba. Shi ya koya wa talakawa da masu neman ’yanci yadda za su nemi hakki ba tare da an zubar da jinji ba, shi ya sa har gobe ba a taba mantawa da shi a Indiya. Haka ma Martin Luther da Malcolm d a Amurka. Su kuwa su Bokassa da Salasie, wasu ma sun fara mantawa da su, ba don komi ba, sai don sun yi shigar shantun }adangare ne a cikin mulki, ba su raga wa jama’arsu ba, don haka tarihi bai raga masu ba har cikin kabari.
Saboda haka muna iya cewa, talakawa su ne ke gina mutum a cikin tarihi, su kuma yi watsi da shi a cikin tarihin, idan bai kasance wanda yake tattare da su ba. Dukkan shugaban da ya kasance yana tattare a kullum da masu tursasa wa talaka da cin mutuncin talaka, to, shi kuma tarihi ba zai daina tursasa masa ba, ba kuma zai daina cin mutuncinsa ba, har sai ya dawo cikin tsari da tunani na so da kuma yin aiki ga talaka. Duk wani abu da ba haka ba, aikin baban giwa ne. Talaka a halin yanzu ya waye fiye da yadda ake tunani, ba wani mai mulki ko son mulki da zai tursasa masu, ya ce masa ga yadda zai yi ko inda zai bi. Lokaci ya yi da masu han}oron cin talaka da buguzum za su san cewa kifi na ganin mai jar koma.