Shugabanni su daina sanya siyasa kan matsalar rashin tsaro – Tambuwal

Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bukaci shugabannin siyasa su daina sanya siyasa a cikin matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan.Alhaji Aminu Tambuwal ya bayyana haka ne lokacin da yake ba da taimakon jini ga wadanda harin bam na Nyanya da ke wajen Abuja ya shafa a ranar Litinin da ta […]

Shugabanni su daina sanya siyasa kan matsalar rashin tsaro – Tambuwal

Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bukaci shugabannin siyasa su daina sanya siyasa a cikin matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan.
Alhaji Aminu Tambuwal ya bayyana haka ne lokacin da yake ba da taimakon jini ga wadanda harin bam na Nyanya da ke wajen Abuja ya shafa a ranar Litinin da ta gabata, inda fiye da mutum 70 suka mutu. Ya ce “A matsayinmu na shugabanni a wannan kasa, wajibi ne mu hada kai mu tallafa wa gwamnati wajen magance wannan kalu-bale. Mu daina sanya siyasa a cikin lamarin rashin tsaro. Daga abin da na gani a wurin wadanda aka kai wa harin ina shakku a a ce sun fito ne daga wata jam’iyyar siyasa. Wajibi ne mu magance lamarin, kuma bai da alaka da wani addini.”
Tambuwal ya nuna zai bayar da taimakon jinin ne lokacin da ya ziyarci wasu daga cikin wadanda harin ya shafa a Asibitin kasa da ke Abuja, inda daga baya ya tafi cibiyar adana jini ta kasa domin bayar da taimakon jinin.
Ya ce yana da muhimmanci a nuna kauna da kula ga wadanda harin ya rutsa da su inda ya bukaci ’yan Najeriya su tallafa wa gwamnati a kokarinta na magance matsalar rashin tsaro. “Kuma ina kira ga jama’a da suke da wadataccen jini su yi kokari su je su ba da taimakon jini, kuma su yi duk abin da ake bukata domin ceto rayukan wadanda harin ya shafa.”
A lokacin ziyarar Tambuwal shi ma Ministan Lafiya Farfesa Onyebuchi Chukwu ya rika zagayawa yana gaida wadanda harin ya rutsa da su.
Mutane da dama sun rika kai taimakon jini domin ba wadanda harin ya shafa daga cikinsu akwai Sanata Bukola Saraki daga Jihar Kwara.