Shugabanni su dauki darasi daga matsalar da ta samu jirgin Kabo a Sakkwato – Limami

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Life Camp da ke Abuja, Imam Idris Shu’aibu,  ya shawarci shugabanni da kamfanonin jiragen sama a kasar nan su dauki darasi daga matsalar da ta samu jirgin saman Kabo a Sakkwato, inda ya yi saukar gaggawa ranar Juma’ar da ta gabata a kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya.Imam Idris Shu’aibu ya […]

Shugabanni su dauki darasi daga matsalar da ta samu jirgin Kabo a Sakkwato – Limami
Shugabanni su dauki darasi daga matsalar da ta samu jirgin Kabo a Sakkwato – Limami

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Life Camp da ke Abuja, Imam Idris Shu’aibu,  ya shawarci shugabanni da kamfanonin jiragen sama a kasar nan su dauki darasi daga matsalar da ta samu jirgin saman Kabo a Sakkwato, inda ya yi saukar gaggawa ranar Juma’ar da ta gabata a kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya.
Imam Idris Shu’aibu ya bayyyana haka ne ga wakilinmu na Bauchi, inda ya ce mutane sun kasance a filin jirgin saman Kano na tsawon kwanaki suna jiran jirgin Kabo ya dauke su zuwa aikin Hajji a ranar har mutane sun shiga jirgin zai tashi, sai ma’aikatan jirgin suka shigo cikin jirgin suka ce za a rage mutum 30, ba tare da sun bayar da wani dalili ba.  “Kasancewar kowa ya zauna a kujerarsa za a tashi, sai kowa ya yi shiru, sai suka nuna wani adadi na kujeru suka ce su sauka kurum za a sanya su a jirgin gobe,” inji shi.
Imam Idris ya ce kujerarsa ta kasance cikin wadanda aka umarci su sauka ganin haka shi da wasu malamai suka yi ta rarrashin mutanen da abin ya shafa wasu suka amince suka fara sauka amma wasu suka ce ba za su sauka ba, kamar za a nuna musu karfi, don haka suka lallabi wadanda abin ya shafa da kyar suka sauka. Amma wani dattijo sai ya fashe da kuka ya ce kwanansa biyar yana kwana a filin jirgi yaya za a yi masa wannan cin mutunci, to, shi bai yafe ba sai Allah Ya saka masa, suka ce an ji ya dai sauka, yana kuka ya sauka daga jirgin.
Limamin ya ce sai bayan sun sauka aka ba su labarin cewa Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Sa’idu Nasamu dakingari ne bayan an gama shigar da mutane ya nemi alfarmar a sama masa wuri a cikin jirgin shi da matarsa da tawagarsa ta mutum 40 a jirgin alhali bai fi saura kujera 10 ba don haka suka ce dole a saukar da mutum 30 kuma aka yi hakan.
Imam Idris ya ce duk da haka sun yi ta ba junansu hakuri kuma ba su yi mummunar addu’a ba amma akwai wadanda suka ce ba su yafe ba, saboda haka da aka ba su dakuna a Green Desert Farm Hotel su 23 suka je suka kwanta amma sauran mutanen bakwai duk sun yi zuciya kowa ya kama gabansa sun ce ba za su je ba saboda takaici.