Shugabanni sun yi taron hada kan al’ummar Arewa a Benin
Shugabannin alummar Arewa mazauna garin Benin a Jihar Edo sun yi wani taro na musamman inda suka tattauna a kan hanyoyin da suka dace su bi domin samar wa ’yan Arewa maslaha a kan matsaloli da suka dade suna ci musu tuwo a kwarya game da zamansu a Benin.Taron wanda aka gudanar a Zangon Eyaen, […]

Shugabannin alummar Arewa mazauna garin Benin a Jihar Edo sun yi wani taro na musamman inda suka tattauna a kan hanyoyin da suka dace su bi domin samar wa ’yan Arewa maslaha a kan matsaloli da suka dade suna ci musu tuwo a kwarya game da zamansu a Benin.
Taron wanda aka gudanar a Zangon Eyaen, Shugaban ’yan Arewa mazauna Benin Alhaji Badamasi Sale ne ya jagorance shi, inda a jawabinsa ya ce taron na neman hada kan al’ummar Arewa mazauna garin Benin da Kudu ne baki daya.
“Akwai matsaloli da dama da suke addabar ’yan Arewa mazauna nan Kudu da ya zama tilas mu shugabanni mu hada kai kuma mu tashi tsaye mu nemi hanyar magance su a hukumance ba tare da wani ya dauki doka a hannu ba. Kuma hanyar ita ce mu samar da kyakkyawar fahimta da hadin kai a tsakanin ’yan Arewa da suke zaune a nan Kudu, wannan zai ba mu karfin gwiwar tunkarar kowane kalubale da ke gabanmu kuma mu kai damuwarmu wurin hukuma ta saurare mu domin idan da hukuma na ciki za mu samu maslaha,” inji shi.
Shugaban ya ce taron shiyyoyi uku da suke da su, gaba dayan shugabanninsu 20 sun halarce shi kuma sun ba da goyon baya da hadin kai na su tashi tsaye su yi wa al’ummar Arewa da suke jagoranta aiki cikin gaskiya da adalci.
Da dama daga cikin shugabannin sun tofa albarkacin bakinsu a wurin taron inda suka tabo batutuwa masu muhimmanci dangane da harkar rayuwa, kuma abin da ya fi daukar hankali a lokacin shi ne batun rikicin manoma da makiyaya a jihar da kuma masu rabewa da sunan aikin kura- kura suna tafka barna sai kuma ’yan gwangwan da wasu daga cikinsu ke wuce gona da iri da kuma masu talle a cikin garin Benin da kewaye wadannan gaba daya sun ce suna kawo matsaloli a wasu lokuta don haka za a dauki matakin tantance irin wadannan batagari, inji shugabannin.