Shugabannin addini ga masu zabe: Mutuwa domin wani asara ce
A gobe idan Allah Ya kai mu ne ake sa ran za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya. Domin tabbatar da an gudanar da zaben lami lafiya ba tare da an samu wata hatsaniya ba a lokacin zaben ko kuma bayansa ne ya sanya Aminiya ta tuntubi shugabannin addinin musulunci […]

A gobe idan Allah Ya kai mu ne ake sa ran za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya. Domin tabbatar da an gudanar da zaben lami lafiya ba tare da an samu wata hatsaniya ba a lokacin zaben ko kuma bayansa ne ya sanya Aminiya ta tuntubi shugabannin addinin musulunci da na kirista domin su jawo hankalin matasa da ‘yan siyasa game da hadarin da ke tattare da kashe wani ko nakasa wani a sanadiyyar zaben. Inda aka tattauna da Sheikh Sani Yahaya Jingir da Archibishop Ignatius Kaigama da ke Jos da kuma Sheikh Abubakar Tureta da ke Kaduna. Ga bayanin da suka yi:
Matasa ku yi taka-tsantsan -Sheikh Jingir
Shugaban Majalisar malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir. A wannan tattaunawar da ya yi da wakilinmu ya bayyana cewa akwai babban nauyi kan matasa na ganin an yi zaben da za a gudanar gobe lafiya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya; Wane kira kake da shi ga matasa dangane da guje wa tada rikice rikice a lokacin wannan zabe?
Sheikh Jingir; To, ina kira ga matasa su sani akwai babban nauyi a kansu a lokacin wannan zabe wajen ganin an yi zaben nan lafiya, don haka su yi taka-tsantsan su zamanto masu sauraron nagaba da su. Muna fata Nijeriya ta fita daga cikin matsalolin da take ci. Muna kira ga ‘yan Nijeriya kowa ya bada gudunmawarsa don ganin an yi wannan zabe lafiya. Kuma ina kira ga hukumomin tsaro na soja da ‘yan sanda da ‘yan agaji su yi ayyukansu don Allah. Kada su razana jama’a, a yi zaben lafiya, a zabi mutanen da za su ceto kasar nan daga halin da muke ciki.
Aminiya; Yaya matsayin mutumin da ya kashe wani ko ya kashe kansa ko ya raunata wani ko ya raunata kansa kan wani dan siyasa a addinin musulunci?
Sheikh Jingir; Allah Ya haramta kisan kai ga al’ummar musulmai. A addinin musulunci wanda ya kashe wani shi ma hukuma za ta kashe shi, bayan an yi bincike an tabbatar da ya aikata wannan laifi. Haka wanda ya kashe kansa da kansa ya auka cikin babban zunubi. Annabi Muhammad (SAW) ya nuna cewa daga cikin azabar da za a yi wa wanda ya kashe kansa da kansa irin hanyar da ya bi ya kashe kansa da ita za a yi masa azaba a ranar tashin alkiyama. Kuma wanda ya kashe wani haka kawai ba tare da an yi masa hukumci ba, girman zunubin wanda ya aikata haka ya kai, kamar ya tara mutanen duniya ne ya kashe su. Saboda haka Allah Ya hana mutum ya kashe kansa ko ya kashe wani ko ya raunata wani ko ya raunata kansa, haramun ne. Don haka bai hallata matasa su yi fadace-fadace kan wani dan siyasa wanda zai kai ga rasa rayukansu ko yin sanadin rasa rayukan wadansu ba.
Aminiya; Ina matsayin irin ‘yan siyasar nan da suke daukar alkawari lokacin yakin neman zabe amma idan aka zabe su ba sa ciki alkawuran da suka yi?
Sheikh Jingir; To, dangane da maganar alkawari Allah yana cewa ku cika alkawari, lallai alkawari ya kasance wanda da za a yi wa dan adam tambaya a kansa a ranar tashin alkiyama. Akwai alkawari da mutum yake dauka tsakaninsa da Ubangijinsa, akwai alkawarin da mutum yake dauka tsakaninsa da mutane. Lalllai ne mutum ya cika dukkan alkawarin da ya dauka domin za a tambaye shi a ranar tashin alkiyama. Abin da mutum ya san ba zai yi ba kada ya dauki alkarin cewa zai yi, domin idan mutum ya yi alkawarin zai yi wani abu ko ya cika ko bai cika ba akwai hukumci a kansa. Saboda haka da dan siyasa da wanda ba dan siyasa ba a ka’idar musulunci alkawari doka ce wadda dole ne a cika shi. Duk wanda aka ba shi shugabancin jama’a ko shugabancin karamar hukuma ko jiha ko kasa baki daya ya zama dole ya cika alkawarin da ya yi wa jama’a.
Aminiya; Wane sako ne kake da shi dangane da wannan zaben na gobe?
Sheikh Jingir; Ya zama wajibi ga al’ummar Najeriya mu taru mu ji tsoran Allah, mu yi komai don Allah, mu hadiye kwadayi mu zabi wanda zai albarkaci kasar nan, don kasar ta bunkasa da ilmi da karfin tattalin arziki da lafiya da zaman lafiya da cigaba.
Mun gaji da rikice-rikicen siyasa a Najeriya
– Archibishop Kaigama
Hussaini Isah Daga Jos
Archibishop na darikar katolika na Jos kuma shugaban bishop-bishop na darikar katolika a Nijeriya Archibishop Ignatius Kaigama. A tattaunawar da ya yi da wakilinmu ya bayyana cewa an gaji da rikice-rikicen da suke tasowa dangane da siyasa ko addini ko kabilanci a Nijeriya. Don haka ya bukaci al’ummar Nijeriya su hada kansu su gudanar da zaben da za a yi lafiya ba tare da wani tashin hankali ba. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Yaya matsayin wanda ya kashe kansa ko ya kashe wani ko ya raunata wani ko kuma ya raunata kansa kan wani dan siyasa a addinin kirista?
Archibishop Kaigama; Duk mutumin da zai yarda ya bayar da ransa kan wani dan siyasa da yake takarar wani matsayi za a iya cewa ba mai tunani ba ne. Siyasa ta wadanda suke raye ne, wanda ya kashe kansa a banza ina amfanin siyasar a gare shi?. Don haka muna kira ga mutane a yi siyasa ta cigaba, a yi siyasa domin a daukaka dan’adam, a yi siyasar da za ta kawo zaman lafiya don a samu cigaba a ci moriyar irin albarkatun da Allah Ya hore mana a Najeriya. Kuma duk wanda ya shiga siyasa ya sani ya shiga ne domin ya yi gyara, ya sada zumunci, ya yi sanadin yadda al’umma za ta ci arzikin da Allah Ya bai wa kasa ta yadda ba za a samu talauci a cikin kasa ba, ba za a samu masu yunwa da ciwo ba. Ya gyara hanyoyi, ya samar da makarantu. Wannan shi ne amfani da darajar siyasa.
Aminiya; Wanne kira ko jan hankali ne kake da shi zuwa ga matasa dangane da guje wa tashin hankali a lokacin wannan zaben?
Archibishop Kaigama; Mun gaji da rikice-rikicen da suke tasowa dangane da siyasa ko addini ko don kabilanci a Nijeriya. Mun gaji da wadannan abubuwa. Sauran kasashen duniya suna ta cigaba, kasashen da suka taso a bayan Najeriya suna ta cigaba saboda sun hada kai komai yana tafiya daidai.
A irin wadannan kasashe kowa yana tunanin irin gudunmawar da zai bayar ne wajen cigaban kasarsa. Amma mu kowa ya kebe kansa yana cewa wannan iyalisa ne ko wannan yarensa ne ko wannan ‘yan addininsa ne. Irin wadannan abubuwa ba za su taba kawo mana cigaba a Nijeriya ba. Don haka ya kamata ‘yan Nijeriya mu yi tunani, ya kamata siyasa ta kawo mana cigaba a Nijeriya ba tashe-tashen hankula ba.
Bai kamata idan siyasa ta zo a yi amfani da kudade don a danne hakkin mutane don kada a yi zaben gaskiya ba. Don haka muna kira ga ‘yan siyasa mu yi siyasa da tsoran Allah, kada mu yi siyasar zamba, kada mu yi siyasar cutar al’umma, mu yi siyasar da za ta kawo mana cigaba.
Aminiya; Me za ka ce kan irin ‘yan siyasan nan da suke yi wa al’umma alkawura a lokacin yakin neman zabe, amma idan aka zabe su sai su ki cika alkawuran da suka yi?
Archibishop Kaigama; To, masu iya magana suna cewa alkawari kaya ne, wanda ya yi alkawari bai cika ba ya zama yana zaune da wannan kaya na alkawari da ya yi wa al’umma har zuwa ranar tashin alkiyama. Saboda haka gara ka ki daukar al’kawari a maimakon ka dauki al’kawarin da ba za ka cika ba, domin duk mutumin da ya dauki alkawari bai cika ba, to ya saba wa Allah, ya saba wa mutane. Kuma duk wanda aka zaba a wani matsayi bayan ya yi rantsuwa da Baibul ko Alkura’ani ya ce zai yi wa mutane aiki da kudadensu da aka ba shi, amma da ya shiga ya ga kudi ya yi yawa sai ya manta da cewa ya yi rantsuwa, ya yi alkawari, to ya sani Allah bai manta ba.
Aminiya; Wane sako kake da shi zuwa ga al’ummar Najeriya dangane da wannan zabe da za a gudanar?
Archibishop Kaigama; To, a kullum muna addu’a Allah Ya sa mu yi zaben nan lafiya, wanda ya ci a ba shi, wanda bai ci ba ya yi hakuri ya rungumi wanda ya ci. Su kuma masu son tayar da zaune tsaye a lokacin wannan zabe, Allah Ya shirye su, Ya sanya ruwa mai sanyi a zuciyarsu, su yi hakuri da wannan buri nasu. Su sani cewa tayar da hankalin jama’a ba zai taimake mu ba, mu yi hakuri mu yi zaben nan lafiya, a bai wa wanda ya ci.
Cigaba a shafi na 3