Shugabannin Afghanistan da Amurka sun gana don farfado da dangantaka

Shugabannin Afghanistan a karkashin jagorancin Shugaban kasar Malam Ashraf Ghani sun gana da Shugaban Amurka Mista Barack Obama don farfado da dangantaka a tsakanin kasashen biyu. Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani da babban jami’in harkokin mulkin kasar Malam Abdullah Abdullah sun gana da kusoshin gwamnatin Amurka a fadar hutu ta Shugaban Amurka da ake kira Camp […]

Shugabannin Afghanistan da Amurka sun gana don farfado da dangantaka
Shugabannin Afghanistan da Amurka sun gana don farfado da dangantaka

Shugabannin Afghanistan a karkashin jagorancin Shugaban kasar Malam Ashraf Ghani sun gana da Shugaban Amurka Mista Barack Obama don farfado da dangantaka a tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani da babban jami’in harkokin mulkin kasar Malam Abdullah Abdullah sun gana da kusoshin gwamnatin Amurka a fadar hutu ta Shugaban Amurka da ake kira Camp Dabid da ke Jihar Maryland da ba ya da nisa da birnin Washington a ranar Litinin.
Tattaunawar wadda ta hada da Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry da Sakataren Tsaron Amurka Ashton Carter da kuma Sakataren Baitul Mali, Jack Lew, an gudanar da ita ce domin inganta danganatakar aiki a tsakanin kasashen biyu, wacce ta yi tsami saboda shekara 14 da Amurka ta yi tana yaki a kasar da kuma zaman doya da manja da aka samu a tsakanin Amurka da tsohon Shugaban Afghanistan Hamid Karzai.
A lokacin da suka yi shawarwarin shugabannin sun yi kokarin su yi magana kan batun tsaro da Shugaba Ashraf Ghani ya nuna. Sakataren Tsaron Amurka Ashton Carter ya ce Amurka za ta bukaci karin kudi domin tabbatar da karfin sojojin Afghanistan ya dore kan dakaru dubu 352, har zuwa shekarar kudi ta 2017.
Sakatare Carter ya ce kwamandojin sojojin taron dangi da kwamandojin Afghanistan sun bada shawarar a tabbatar da karfin jami’an tsaron kasar domin rage su zai maida hannun agogo baya a nasarori da aka samu ta fuskar tsaro.
Daga bisani shugabannin sun yi taro da manema labarai domin bayyana abin da suka kira “farfado da dangataka tsakanin kasashen biyu.”