Shugabannin Afirka sun bukaci taimakon NATO kan rikicin Libya
Shugabannin Afirka sun yi kira ga kungiyar kawancen Tsaro ta NATO da sauran kasashen Yammacin Duniya da su taimaka wajen kawo karshen rikicin kasar Libya da kuma takaita bazuwar rikicin zuwa sauran kasashe makwabta. Shugabannin sun yi wannan kiran ne a kasar senegal ranar Talata lokacin wani taro na kasashe da ke makwabtaka da kasar […]
Shugabannin Afirka sun yi kira ga kungiyar kawancen Tsaro ta NATO da sauran kasashen Yammacin Duniya da su taimaka wajen kawo karshen rikicin kasar Libya da kuma takaita bazuwar rikicin zuwa sauran kasashe makwabta.
Shugabannin sun yi wannan kiran ne a kasar senegal ranar Talata lokacin wani taro na kasashe da ke makwabtaka da kasar Libya. rikici ya barke a kasar ne tsakanin dakaru masu goyon bayan Firaministan kasar, Abdullah al-Thinni da kuma dakuru masu kishin Islama wadanda suke barazana ga kasashe makwabta kamarsu: Chadi da Nijar da Mali da kuma Burkina Faso.
A lokacin da yake jawabi Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar keita ya ce: “Matukar ba mu kawo karshen rikicin da ke ruruwa akudancin Libya ba, to ba za a taba samun zaman lafiya a baki dayan yankin ba,” inji shi.
A nasa bangaren Shugaban Idriss Deby ya ce: “Lalubo hanyar kawo karshen wannan rikicin ba ya hannun ’yan Afirka, amma a hannun kasashen Yamma musamman ma kungiyar NATO. A yanzu kasar Libya ta zama wani wuri na bai wa ’yan ta’adda horo, kuma ya wajaba ga NATO ta dakatar da hakan.”
Amma kasashen sun zargi Yammacin Duniya da yin biris da su, kuma tun bayan kisan Muammar Gaddafi NATO ta fice daga kasar, inda aka bar su su tafiyar da ita da kansu.
kasar Mali dai ita ce kasar da rikicin Libya ya fi shafa. Kuma rikicin ya barke ne bayan hanbarar da marigayi Shugaba Gaddafi lokacin da wasu da suke da alaka da kungiyar al-kaeda suka kwashe makamai daga rumbun adanasu, inda suka karbe iko da arewacin a shekarar 2012. Kodayake, wani kawance da kasar Faransa ta jagoranta ya fatattaki ’yan gwagwarmayar daga wuraren da suka kame, amma hakan ya sa su akaddamar da hare-haren musamman akan dakarun Mali da ke aikin kiyaye zaman lafiya a kasar.