Shugabannin Afirka sun ‘shelanta yaki’ da Boko Haram

kasashen Afirka da suka gudanar da taro kan tsaro a Paris tta kasar Faransa sun cimma matsaya domin hada hannu wajen yaki da kungiyar Boko Haram.A lokacin taron da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata, kasashen da ke makwabtaka da Najeriya sun shelanta yaki da Boko Haram, inda suka sha alwashin hada karfi […]

Shugabannin Afirka sun ‘shelanta yaki’ da Boko Haram
Shugabannin Afirka sun ‘shelanta yaki’ da Boko Haram

Shugabannin da suka halarci taron zaman lafiya na Faransakasashen Afirka da suka gudanar da taro kan tsaro a Paris tta kasar Faransa sun cimma matsaya domin hada hannu wajen yaki da kungiyar Boko Haram.
A lokacin taron da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata, kasashen da ke makwabtaka da Najeriya sun shelanta yaki da Boko Haram, inda suka sha alwashin hada karfi da Najeriya domin ganin bayan kungiyar.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito Shugaban Jamhuriyar Chadi Idriss Deby yana cewa, kasashen yankin sun yanke shawarar “kaddamar da yaki kan Boko Haram.” Yayin da Shugaban Jamhuriyyar Kamaru Mista Paul Biya ya yi magana da kakkausar murya cewa: “A nan mun shelanta yaki a kan kungiyar Boko Haram,” Biya ya bayyana haka ne ga manema labarai bayan kammala taron.
A ranar Juma’ar da ta gabata, mayakan da ake zargi na Boko Haram ne sun kai hari ga wani sansanin ma’aikata ’yan kasar China da ke aikin hanya a Arewacin Kamaru. Kuma gwamnan yankin ya ce mayakan sun sace mutum 10. Shi kuma babban jami’in ’yan sandan yankin ya ce an kashe mutumin China daya a harin.
Shugaban Faransa Francois Hollande ya kira taron na Asabar ne, bayan sace ’yan matan. Kuma shugabannin kasashen Benin da Kamaru da Chadi da Faransa da Nijar da Najeriya ne suka halarce shi. Ministan Harkokin Wajen Birtaniya, William Hague da jami’an kasar Amurka ma sun halarci taron.
Kuma a yayin da masana diplomasiyya suka ce kasashen Turai da Amurka ba za su sanya sojojinsu su fafata ba, kasashen Yamma suna bayar da shawarwari da tallafi ga Najeriya.
Hollande ya ce, “Akwai bukatar a samar da musayar bayanai don tsara matakin dauka da kuma kula da kan iyakoki.”
Shi kuwa Hague ya ce Birtaniya za ta bayar da shawarwari ga sojojin Najeriyya. “Jami’an tsaron Najeriya ba a tsara su don irin wannan lamari ba, wannan ne ya sa matsalar ke kara baci,” Hague ya shaida wa manema labarai a Paris ranar Asabar.
Ya kara da cewa, “Najeriya ke da babban nauyi, kuma ita ce za ta jagoranci sauran kasashe wajen fuskantar wannan da wancan, ciki har da samar da dabarun tsaro da kuma samar da ci gaba.”
Kamfe din da aka rika yayatawa ta kafar sadarwa ta tiwita mai taken: “A dawo mana da ’yan matanmu,” ya samu goyon bayan kasashen duniya don gano ’yan matan da aka sace daga makaranta. Zuwa yanzu kasashen Faransa da Biratniya da Isra’ila da Spain da Amurka sun yi alkawarin samar da mashawarta da jiragen yaki na leken asiri da kuma bayanan sirri domin taimaka wa Najeriya wajen gano inda ’yan matan suke.