Shugabannin APC na ci gaba da zawarcin Gwamnonin G-7

Shugabannin Jam’iyyar APC sun ci gaba da zawarcin kungiyar Gwamnoni Bakwai da ake kira G-7 a daidai lokacin da rikicin cikin gida ke ci gaba da zafafa a Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan. Shugabannin na APC da suka hada da shugaban jam’iyyar ta kasa Ci Bisi Akande da Janar Muhammadu Buhari da Cif Bola […]

Shugabannin APC na ci gaba da zawarcin Gwamnonin G-7
Shugabannin APC na ci gaba da zawarcin Gwamnonin G-7

Shugabannin Jam’iyyar APC sun ci gaba da zawarcin kungiyar Gwamnoni Bakwai da ake kira G-7 a daidai lokacin da rikicin cikin gida ke ci gaba da zafafa a Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan.

Shugabannin na APC da suka hada da shugaban jam’iyyar ta kasa Ci Bisi Akande da Janar Muhammadu Buhari da Cif Bola Tinubu sun ziyarci gwamnonin jihohin Neja da Ribas a ranar Litinin da Talatar da suka gabata.
A Ribas mai masaukinsu Gwamna Rotimi Amaechi ya ce zai tuntubi jama’ar jihar da na yankin Kudu maso Kudu kafin ya amshi tayin Jam’iyyar APC nay a koma cikinta.
Amaechi wanda ke takun-saka da jam’iyyarsa ta PDP ya bayyana masu kokarin ganin bayansa a matsayin gurbatattu da karfin jama’a masu tunanin ne kawai za sudakile su.
Gwamna Amaechi ya ce, “A ranar da za mu yanke shawara, za ta kasance ne a sabon filin wasanmu da zai dauki mutum dubu 40. Tinubu da shugabab kasa (Buhari) za su yi jawabi ga mutum dubu 40. Don haka akwai bukatar mu je kara kirar jama’a. Suna da kudi suna da ’yan sanda, suna da soja, abin da kawai muke da shi,shi ne jama’armu.”
A jawabin Cif Bisi Akande bayan yaba wa jajircewar Gwamna Amaechi ya neme shi ya jagorancin jama’arsa zuwa APC, inda ya ce “Masu ra’ayin ci gaba sun taho da jirgin fito. Wannan yunkuri ne na ceto Najeriya.”
A nasa jawabi Janar Buhari ya ce “Mun zo nan ne domin neman fahimta da goyon bayanku ta hannun jagoranku Gwamna Amaechi. Na yi aiki da daya daga cikin manyan jarumanku Farfesa Tam Dabid West.
A Minna Gwamnan Jihar Neja, Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ya shawarci jiga-jigan na Jam’iyyar APC su ziyarci sauran gwamnonin kasar nan a kokarin da suke yi na samun mutanen da suke da akidar samar da canji mai tasiri a kasar nan.
Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ya bayar da shawarar ce a lokacin da tawagar ta kai masa zawarci a maraicen Talatar da ta gabata,ya ce,bai kamata mutane su zura ido wadansu mutane suna abubuwan da suka saba wa tanadin da jam’iyyar ta yi,sannan a rufe baki a yi shiru tare da nade hannu ba.
Gwamnan ya ce ko kadan babu kashin gaskiya a labaran da ake fadin cewar yana da shirin barin gungun Gwamnoni bakwai da suka lashi takobin ganin an gyara kura-kuran da aka tabka da ya kai su ga kafa sabuwar PDP.
Tsohon Shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari ya jinjina wa gwamnonin da suka dauki matakin ganin an daidaita sahu a jam’iyyarsu. Ya ce wannan alama ce da ke nuna kan mutane ya kara wayewa game da irin wainar da ake toyawa a fannin siyasa.
Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Cif Bisi Akande, ya ce jam’iyyar, muddin ta kafa gwamnati za ta samar da ingantaciyyar rayuwa, sabanin halin da jama’a suka fada fiye da shekara 14 na mulkin PDP.