Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa

Shugabannin sun tattauna batutuwa da suka shafi jam’iyyar da kuma nemo musu da mafita.

Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa

Shugabannin Jam’iyyar APC, ciki har da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni, da sauran manyan jagorori, sun gana a daren Talata a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

An gudanar da taron ne domin shirye-shiryen babban taron jam’iyyar na ƙasa da za a yi a yau a hedikwatar APC.

Wannan shi ne taron farko da za a yi taron tun bayan hawan Shugaba Tinubu kan mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

A bara, an tsara shirya waɗannan taruka ne a watan Satumba, amma aka ɗage su ba tare da saka sabuwar rana ba.

A baya-bayan nan, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya soki shugabannin jam’iyyar da rashin shirya taruka, inda ya ce APC ta fara rabuwa da aƙidun da aka gina ta a kai.

An fara taron ne da misalin ƙarfe 7:30 na dare, bayan isowar Shugaba Tinubu.

Batutuwan da aka tattauna sun haɗa da shirin gudanar da babban taron jam’iyyar, matsalolin shari’a da ke shafar jam’iyyar, cibiyar nazari da tsara manufofin APC da sauransu.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Sauran sun haɗa da wasu gwamnoni kamar Hope Uzodinma (Imo), Babajide Sanwo-Olu (Legas), Dapo Abiodun (Ogun), da Babagana Umar Zulum (Borno).

Haka kuma, mambobin kwamitin jam’iyyar da tsohon shugaban APC na ƙasa, Cif Bisi Akande, sun halarci taron.

Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N860 a Legas

Na gaji bashin 8.9bn a matsayin shugaban APC — Ganduje

Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno

Buhari da El-Rufai ba su halarci babban taron APC ba