Shugabannin Arewa a mike tsaye
Wai Mutanen Arewa 486 da aka kama a jihar Abia, haka zikau da sunan ‘ya’yan kungiyar Boko Haram! Wannan cin mutunci har ina? Ina da yakinin ba wata jiha a Arewacin Najeriya da ke tsangwamar al’ummar Kudancin Najeriya da suke jibge a wannan yanki namu mai albarka. A kullum daren Allah ta’ala al’ummarsu kan shigo […]
Wai Mutanen Arewa 486 da aka kama a jihar Abia, haka zikau da sunan ‘ya’yan kungiyar Boko Haram! Wannan cin mutunci har ina? Ina da yakinin ba wata jiha a Arewacin Najeriya da ke tsangwamar al’ummar Kudancin Najeriya da suke jibge a wannan yanki namu mai albarka. A kullum daren Allah ta’ala al’ummarsu kan shigo Arewa, su zauna inda suke so, su yi kasuwancinsu cikin walwala, su yi addininsu duk dai ba tare da mun tsangwamesu ba.
Haka Akwai dimbin ‘yan asalin kudancin Najeriya, wadanda kwata-kwata ba su taba shigowa Arewa ba. Amma su zo a cikin dare daya su cike muna gurabun aikin gwamnati a jahohinmu, misali a jihata ta Zamfara a kusan duk ma’akatar da ka leka sai ka taras da ‘yan Kudancin Najeriya a matsayin ma’aikata, musanman a bangare Ilmi da a nan ne suka fi yin kaka-gida.
Anya! Kuwa mutanen da muka yi wa wannan halaccin, sun cancanci su wulakanta al’ummarmu da ke shiga ‘yankinsu???? Amsa daya tilo ita ce, a’a, amma wani hanzari ba gudu ba, Hausawa sun ce “sai bango ya tsage kadangaru ke samun wajen shiga” domin mu ne da kanmu muka ba su damar, har suke amfani da ita wajen wulakantar da mu a kowane fanni na
rayuwa. Haba ‘yan uwana ’yan Arewa, wai mene ne abin kwadayi ga kitsen rogo???? Har kullum dai yakan kasance marmari ne, amma fa daga nesa domin kusan dukkan wadanda suka dandanashi sukan tabbatar mana da dacinsa.
Duk da mun san da cewa abincin mutun duk inda ya kai, to fa mutun ba zai mutu ba sai ya je can ya ciyo shi. Wannan shi dai ne abin da munka yarda da shi kuma shi ne babban abin da ya sa al’ummarmu ke tururuwa zuwa kudancin. Wanda wallahi in dai ba mu fi su arzikin ba, to wallahi ba za su fi mu arzikin ba.
Don haka ’yan uwana ‘yan Arewa duk da dai cewa mun dade muna sharar wannan mummunan barcin, to ya fa kamata mu farka. Domin abin da mamaki, wai har an wayi gari yau akwai wata makararriyar jiha, wai ita Enugu da duk Bahaushen da ke cikinta sai ya yi rajista,kai ka ce kundin tsarin mulkin kasarmu bai ba mu damar zama a inda muke so a fadin kasarmu, ba tare da tsangwama ba.
Daga karshe ina kira ga shugabanninmu na Arewa da su tashi tsaye, su yi maganin wannan cin kashin da ake yi wa al’ummar yankinsu. Su tabbatar Lallai an dauki kyakkyawan mataki akan wannan rashin mutunci da suke ci gaba da yi mana. Domin an ce kasa daya al’umma daya, amma fa kowa yasan gidan ubansa..
Allah muna rokonKa da ka taimaki al’ummarmu, Ka zaunar da yankin Arewa da kowane lungu da sako na kasarmu lafiya. Ya Allah muna rokonKa da ka kawo jituwa da faminta a tsakaninmu. Allahumma amen.
AbdulMalik Sa’idu Mai Biredi Tashar Bagu ya rubuto makalarsa daga Gusau, Jihar Zamfara, ana iya tuntubarsa ta wayar salularsa: 08069807496.