Shugabannin Arewa na haifar da rabuwar kai wajen zaɓen ’yan takara – Kwankwaso
Tsohon Gwamnan na Kano, ya ce shugabannin ba abin da suke haifarwa face rarrabuwar kai a yankin.
Jagoran Ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga shugabannin Arewa da su daina tsoma baki wajen zaɓen ’yan takarar shugaban ƙasa a Najeriya.
Kwankwaso ya ce shugabannin na amfani da sunan yankin wajen ƙirƙiro matsaloli kawai.
- ’Yan sanda sun ƙwato shanun sata a hannun Lakurawa
- Amarya da tsohon saurayinta sun yi yunƙurin kashe ango
Kwankwaso, ya bayyana cewa irin wannan tsoma bakin yana raba kan al’umma, kuma yana haifar da zaɓen shugabannin da ba su cancanta ba.
Yayin wata hira da BBC Hausa, ya shawarci waɗannan shugabanni da su daina tursasa wa al’umma ra’ayinsu kuma su yi koyi da darusan da suka samu daga zaɓukan da suka gabata.
“Irin wannan rashin adalcin yana raba kan jama’a. Duk abin da za ka yi, ka yi shi bisa adalci da gaskiya.
“Hakan bai dace da waɗannan dattawan ba, wasu daga cikinsu iyayenmu ne ko ’yan uwammu, musamman a yankin Arewa maso Yamma, su nuna son kai wajen zaɓen ’yan takara,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “Wani lokaci suna ƙirƙirar ƙaryace-ƙaryace, suna tara mutane kaɗan, su ce wai Arewa ta amince da wasu ’yan takara.
“Amma a zahirin gaskiya mutane biyu ko uku ne kawai ke ƙirƙirar wannan magana don biyan buƙatarsu.
“Maimakon su tafi Abuja ko Fatakwal don tallata mu a matsayin ’ya’yansu, sai suka zaɓi nuna bambanci.”
Kwankwaso ya kafa misali da zaɓen 2019, inda ya ce akwai ’yan takara da yawa da suka cancanta daga Arewa maso Yamma, amma aka yi biris da su saboda irin wannan tsoma bakin.
“Muna da tsofaffin gwamnoni, ministoci, da sauran mutane masu ƙwarewa, amma a ƙarshe sun murɗe zaɓen don biyan buƙatunsu,” in ji shi.
A kwanakin baya, Kwankwaso ya ƙaryata jita-jitar cewa ya yi wata yarjejeniya da Atiku Abubakar da Peter Obi kan yadda mulki zai gudana a tsakaninsu.
Ya ce, “Na ji cewa mutanen Atiku suna gudanar da taruka da shugabannin Arewa da malamai suna yaɗa ƙaryar cewa an yi wata yarjejeniya.
“Abin takaici ne a ga dattawa suna ƙirƙirar abin da bai taɓa faruwa ba.”
Kwankwaso ya bayyana cewa, an yaɗa wannan jita-jitar ne cewa, Atiku, da Peter Obi sun amince za su yi mulki a tare.
“Har sun tara malamai kusan 45 sun faɗa musu wannan ƙarya—wai Atiku zai yi mulki na shekaru huɗu, ni kuma zan yi mulki na shekaru huɗu, sai Peter Obi ya yi mulki na shekaru takwas. Wannan ba gaskiya ba ne,” in ji shi.