Shugabannin Arewa sun bukaci Buhari ya kori hafsoshin tsaro

Rahoton shirin Boko Haram na kai hari a Abuja ya isa zama hujja —CNCE

Shugabannin Arewa sun bukaci Buhari ya kori hafsoshin tsaro

Shugabannin yankin Arewa ta tsakiya a Najeriya sun bukaci Shugaba Buhari ya kori manyan hafsoshin tsaro saboda gazawarsu wajen samar da bayanan sirri.

Gamayyyar dattawan yankin karkashin inuwar (CNCE) ta ce kiran ya zama dole saboda rahoton hukumar kwastam da ke cewa mayakan Boko Haram sun yi sansanonmi a yankin da nufi kai hare-hare hare a Abuja.

“Muna bakin cikin cewa babu jihar Arewa ta tsakiya da ba ta fama da hare-haren ‘yan ta’adda ko kashe-kashe, alhalin a bayan an san yankin da zaman lumana,” inji kungiyar.

Shugaban CNCE Usman Bida da Sakatarensa Moses Okudu sun ce rahoton hukumar kwastam “shi ne irinsa na farko a tarihin Najeriya” sakamakon gazawar “tara bayanai” daga hukumomin tsaro.

CNCE ta ce rahoton hukumar kwastam na taruwar ‘yan Boko Haram a Abuja ya isa zama hujja a kan gazawar shugabancin tsaron da ke bukatar a fara da sallamar manyan hafsohi kafin komai.

Sanarwar na zuwa ne bayan Rundunar Tsaro ta Najeriya ta sanar da cewa ta riga ta sha gaban masu niyyar kai harin.

Sanarwar da Kakakin Runduanr Tasro, Majanjo Janar John Enenche ta ranar Lahadi ta ce dakarun soji a tsaye suke domin dakile duk wata barazana, ya kuma bukaci mazauna da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da harkokinsu.

Wannan dai ba shi ne karon farko da aka sha yin kira da Shugaba Buhari ya tisa keyar manyan hafsoshin ba, saboda zarginsu da gazawa.

A baya shi da kansa ya yi musu kashedi inda ya ce kokarin da suke yi bai wadatar ba wajen samar da tsaro a kasar, mai fama da hare-haren Boko Haram da barayin shanu da masu garkuwa da mutane da ‘ya fashin daji da rikicin manoma da makiyaya da na kabilanci da masu tayar a kayar baya.