Shugabannin Arewa sun yi taro kan matsalar wutar lantarki

Arewacin Najeriya ya shafe sama da mako guda babu wutar lantarki.

Shugabannin Arewa sun yi taro kan matsalar wutar lantarki

Shugabannin Arewacin Najeriya, sun yi taro a Jihar Kaduna, domin tattauna matsalar rashin wutar lantarki da sauran muhimman ƙalubale da suka addabi yankin.

Taron ya samu jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya.

Dukkanin gwamnonin jihohi 19 na Arewa da wasu sarakunan gargajiya sun halarci taron.

Mai magana da yawun Gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya bayyana cewa, shugabannin sun tattauna kan matsaloli kamar tsaro, tattalin arziƙi, da samar da hanyoyin ci gaba mai ɗorewa.

Gwamna Yahaya, ya jaddada buƙatar haɗin kai a tsakanin yankin don inganta tattalin arziƙi, ta hanyar amfani da albarkatun yankin domin samar da ci gaba mai ɗorewa.

Kazalika, ya nuna damuwa game da rashin wutar lantarki da ake fuskanta a yankin, amma ya nemi a zuba hannun jari a harkar lantarki da hanyoyin samar da makamashi don kaucewa irin wannan matsala a gaba.

Ya buƙaci shugabannin da suka halarci taron da su mayar da hankali wajen fito da sabbin hanyoyin bunƙasa yankin Arewa.

Gwamna Yahaya, ya yi nuni da muhimmancin tallafa wa manoma da kuma farfaɗo da masana’antu domin bunƙasa tsaron abinci da bunƙasa tattalin arziƙi.

Ya kuma bayyana muhimmancin sarakunan gargajiya wajen sulhunta rikice-rikice a tsakanin al’umma.

A jawabinsa na maraba, Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, ya jaddada buƙatar dabarar aiki tare don yaƙar matsalar tsaro, wanda ya ce idan babu tsaro ba za a samu ci gaba ba.

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, wanda ya jagoranci sarakunan gargajiya, ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen samar da zaman lafiya.

Ya kuma buƙaci a yi tattaunawa mai zurfi kan tushen matsalar tsaro, wadda ke da alaƙa da talauci.

Sarkin, ya yaba wa Gwamna Yahaya bisa jajircewarsa na tuntuɓar masu ruwa da tsaki daban-daban da kuma ƙarfafa gwamnonin yankin don ɗaukar matakan da za su shawo kan matsalolin yankin.