Shugabannin babbar kasuwar tumatir ta Benin sun roki Gwamnan Jihar Edo
Shugaban Babban kasuwar tumatir na garin Benin, Alhaji Sani Abdullahi ya yi kira ga Gwamna Kwamared Adams Aliu Oshiomhole na Jihar Edo da ya taimaka ya sa a gyara musu kasuwarsu ta timatir, musamman saboda yanayin da take ciki a halin yanzu. “Kasuwar gaba daya a cakwabe take da laka, babu wurin da za a […]
Shugaban Babban kasuwar tumatir na garin Benin, Alhaji Sani Abdullahi ya yi kira ga Gwamna Kwamared Adams Aliu Oshiomhole na Jihar Edo da ya taimaka ya sa a gyara musu kasuwarsu ta timatir, musamman saboda yanayin da take ciki a halin yanzu. “Kasuwar gaba daya a cakwabe take da laka, babu wurin da za a tsayar da motoci masu dakon kaya daga Arewa don su sauke. Haka nan muna karancin shaguna inda za a ajiye kayan don jin dadin gudanar da harkokin kasuwancinmu”. Inji shi.
Shugaba Alhaji Sani ya yi wannan kira ne tare da roko a wata zantawarsa da wakilin Aminiya a ofishinsa da ke kasuwar a Aduwawa ranar Litinin. “Wannan kasuwar ita ce babbar kasuwar kayan gwari irin tumatir da albasa da kabeji da kankana da sauransu a nan Benin, amma sai ya zama muna fama da matsaloli da dama da suka hada da rashin kyawun yanayi a kasuwar;
karancin shaguna da wurin tsayar da motoci masu kawo mana kaya daga Arewa. Saboda haka muna kira tare da rokon mai girma Gwamna ya taimaka ya sa a gine mana kasuwar cikin tsari na zamani, kamar yadda ya yi a sauran kasuwanni manya da kanana cikin garin Benin da kewayenta. Muna jin dadin yadda yake gudanar da ayyukan masu amfanin al’ummar jihar, kuma muna kaunar wannan kyakkyawar manufar gwamnatinsa ta iso gare mu mu ’yan kasuwar tumatir na ’yan Arewa mazauna Jihar Edo”.
Daga nan kuma sai shugaban ya shawarci ’yan kasuwa ’yan asalin Arewa da su hada kai a kan abin da zai kawo ci gaba ga harkokinsu na yau da kullum a jihar ta Edo da ma sauran jihohin Kudu, musamman saboda kasancewar ’yan kasuwa a matsayin wadanda suke da rawar takawa wajen ciyar da al’umma gaba da kuma karuwar tattalin arzikin kasa.
Haka nan kuma ya shawarci takwarorinsa shugabanni na sauran kasuwanni da su kasance masu ilimi da hangen nesa wajen kokarin su rike girmansu su kasance masu rikon amana da kwatanta gaskiya kuma su ci gaba da tuntubar juna a kai a kai, tare da wayar wa ’yan kasuwa kansu kan duk abin da ya shafi hulda tsakaninsu da gwamnatin kasa da kuma al’ummar cikin kasa da waje.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, mataimakin Shugaban kasuwar, Alhaji dandare Musa ya bayyana matukar damuwa a kan rashin ciniki da ’yan kasuwar suke fama da shi a kasuwar. “A halin da ake ciki cinikin kayan fadama ya fadi warwas, domin kwandon timatir wanda muke sayarwa Naira dubu tara zuwa dubu goma a watanni baya, ya dawo ba ya wuce Naira dubu hudu zuwa dubu uku da dari biyar, alhali ga tsadar kudin sufuri daga Arewa zuwa Kudu”. Inji shi.
Shi ma ya bukaci gwamnati ta tallafa musu a wannan fanni, musamman ta yadda za su tsaya da kafafunsu.