Shugabannin da shaiɗan ya yi wa huɗuba ba sa yin nasara – Obasanjo

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce shugabannin da shaiɗan ya yi wa huɗuba ba za sa yin nasara, yayin da waɗanda Allah Ya zaɓa ne ke yin nasara.

Shugabannin da shaiɗan ya yi wa huɗuba ba sa yin nasara – Obasanjo

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce shugabannin da shaiɗan ya yi wa huɗuba ba za sa yin nasara, yayin da waɗanda Allah ya zaɓa ne ke yin nasara.

Ya musanta cewa da yawan shugabanni na yin abin da Allah Ya tsara, inda ya jaddada cewa wasu shaiɗan ne ke musu huɗuba.

Yayin wata tattaunawa ta yanar gizo mai suna “Boiling Point Arena” a ranar Lahadi, Obasanjo ya ce, “Yawancin shugabanni Allah ne ke ɗora su a kan mulki. Amma ba dukkaninsu ne ke yin nasara ba.

“Shaiɗan ma yana iya ɗora shugabanni a kan mulki. Kuma yawancin waɗannan shugabannin ba sa yin nasara.”

Obasanjo ya ce idan ana so a yaƙi cin hanci a Najeriya, dole ne a fara ta kan shugabanni, kuma hakan na buƙatar jajircewa.

Yana bayyana cin hanci a matsayin matsala mai ƙarfin gaske a tsakanin al’umma.

Ya ce, “Cin hanci kamar babbar riga ce. Idan ka riƙe gefe ɗaya, wani gefen yana faɗuwa. Ba abu ne na rana ɗaya ko gwamnati ɗaya ba; yana buƙatar dagewa kullum da ci gaba da yaƙarsa.

“Idan wata gwamnati ta yi sake, cin hanci zai yawaita,” in ji shi.

 

Har ila yau, ya soki waɗanda suke cikin gwamnati sannan suke ƙara yawan talauci wanda hakan ya jefa miliyoyin mutane cikin tsaka mai wuya.

Amma ya yi kira da a samar da ƙarin tsare-tsare na shugabanci da kyakkyawar gwamnati, wanda a cewarsa haka ne kaɗai zai samar wa talakawa sauƙia halin da ake ciki a ƙasar nan.