Shugabannin duniya na ci gaba da aika wa Trump saƙon taya murna

A lokacin mulkinsa na farko, Mista Trump bai ziyarci Afirka ba.

Shugabannin duniya na ci gaba da aika wa Trump saƙon taya murna

Ɗan takarar Jam’iyyar Republican kuma tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump ne ya lashe zaɓen ƙasar da gagarumin rinjaye wanda ya bashi damar doke abokiyar karawarsa ta Jam’iyyar Democrat, Kamala Harris, wadda ita ce mace ta farko baƙar fata da ta tsaya takarar neman kujerar shugabancin ƙasa a tarihin Amurkan.

Tuni dai shugabannin ƙasashen Duniya suka fara aikewa da saƙon taya ga murna ga Trump bisa ga nasarar shi ta sake lashe zaɓen Amurka.

Shugabannin dai na fatan samun kyakkyawar alaƙa tsakanin ƙasar mafi ƙarfin Dimokuraɗiyya da sauran ƙasashen duniya, a wani yanayi da fargaba ta dabaibaye yiwuwar samar da wasu sauye-sauye a manufofin ƙasar na ƙetare saɓanin yadda ake ƙarƙashin Democrats.

Shugaba Xi Jinping na China da Recep Tayyib Erdogan su ne na farko-farko da suka aike da saƙon taya murnar, inda Xi ya bayyana fatan samun kyakkyawar alaƙa ba tare da tarnaƙi ba tsakanin Beijing da Washington.

Sai shugaba Emmanuel Macron na Faransa wanda ke cewa a shirye ya ke ya yi aiki da Donald Trump kamar yadda suka yi a baya, yayinda Giorgia Meloni ta Italiya da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu suka taya Trump murna bisa sake dawowa da ya yi a shugabancin Amurka.

Shugaban gwamnatin Austria Karl Nehammer ya ce za su yi aiki da Donald Trump domin tunkarar ƙalubalen da duniya ke fuskanta.

A ɓangare guda, Firaministan India Narendra Modi da Ola Sholz na Jamus da kuma shugaban ƙungiyar tsaro ta NATO taya murna suka yi tare da fatan samun alaƙa mai kyau tsakaninsu da Amurka.

Gwamnatin Taliban a Afghanistan na fatan samun “sabon babin dangantaka” bayan sake zaɓen Donald Trump wanda ya rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Taliban a wa’adinsa na farko.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar, Abdul Qahar Balkhi ya bayyana a shafin X cewar yana fatan samun ci-gaba mai ma’ana a dangantakar da ke tsakaninsu.

Firaministan Iraki, Mohamed Chia al-Soudani, ya ce a shirye yake ya ƙarfafa dangantakar ƙasarsa da Washington bisa sharaɗin mutunta juna da cin moriyar juna.

Shi ma shugaban kasar Iraki Abdel Latif Rachid yana fatan sabuwar gwamnatin Amurka za ta karfafa zaman lafiya da tattaunawa mai ma’ana a yankin Gulf. Da ma, gwamnatin Bagadaza na daukar matakan daidaita al’amura na nesanta Iraki daga rikicin yankin Gabas ta Tsakiya, kama daga na Zirin Gaza Hamas har zuwa na Isra’ila da Hezbollah.

Daga Ethiopia zuwa Masar, Afirka ta Kudu zuwa Najeriya, shugabannin Afirka sun taya Donald Trump, murnar nasarar cin zaɓen shugaban Amurka a karo na biyu bayan ya bar mulkin shekara huɗu baya.

Cikin wani saƙo da Fadar Shugaban Najeriya ta fitar, ta ce Shugaba Tinubu na fatan karfafa dangantakar da ke tsakanin Najeriya da kuma Amurka.

A cewar Shugaba Bola Tinubu, nasarar da Trump ya samu na tabbatar da irin amannar da ‘yan kasar suka yi a kansa, musamman wajen gudanar da shugabanci nagari.

Ya kuma yaba wa al’ummar Amurka bisa irin jajircewarsu wajen ba wa tsarin dimokuraɗiyya gudunmawar da ta dace.

Sai dai wasu bayanai na cewa a lokacin mulkinsa na farko, Mista Trump bai ziyarci Afirka ba, abin da ya janyo masa suka kan taƙaitacciyar mu’amala da nahiyar.

Sai dai masu sharhi na ganin wa’adin mulkinsa na biyu ka iya ba shi damar ƙarfafa manufofin Amurka a kan abubuwan da suka shafi Afirka, kamar lafiya da kasuwanci da kuma tsaro.

Haka kuma ana ganin sai Trump ya yi aiki tuƙuru kafin ya iya kawar da tasirin ƙasashe irin su China da Rasha, wadda ta samu shiga Afirka sosai yayin da Amurka ta kawar da kai a kan nahiyar.