Shugabannin ECOWAS na ganawa a Abuja
Ana sa ran bayan kammala taron, ECOWAS za ta fitar da sabon shugabanta.
Shugabannin ƙasashen da ke ƙarƙashin ƙungiyar ECOWAS da wakilansu na ganawa a Cibiyar Taro ta Fadar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja.
Wannan taron shi ne taro na 65 na shugabannin ƙasashen ECOWAS.
- Gwamnati za ta yanka wa hakimai albashi a Sakkwato
- ‘Yan Arewa za su samu albarka a Kasuwar Ogere — Sarkin Ogere
Ana sa ran shugabannin ECOWAS, za su sanar da sabon shugaban ƙungiyar wanda zai jagorancenta na tsawon shekara guda.
Amma hakan zai tabbata ne kawai a ƙarshen taron, wanda aka fara da misalin ƙarfe 12 na rana.
A lokacin shugabancin Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban ECOWAS, an fuskanci juyin mulki a wasu ƙasashen mambobin ƙungiyar.
Hakan ya sanya ECOWAS ƙoƙarin ci gaba da dawo da Nijar, Mali, da Burkina Faso cikin ƙungiyar, bayan a baya sun bayyana ficewarsu daga cikinta.
Duk da ƙoƙarin ECOWAS, ƙasashen sun sake jaddada ƙudurinsu na ficewa daga cikinta.
Idan ba a manta ba, ƙasashe irin su Nijar, Burkina Faso da Mali sun fuskanci juyin mulki daga sojoji, waɗanda suka hamɓarar da gwamnatin fararen hula a ƙasashen.
Hakan ne ya sanya ECOWAS yin barazanar ɗaukar matakin soji musammam a Nijar matuƙar sojoji ba dawo da mulkin demokuraɗiyya a ƙasar ba.