Shugabannin Fulani mazauna Kudu sun musanta samuwar sabuwar rijista
Shugaban majalisar sarakunan Fulani mazauna jihohin Kudu maso yamma kuma sarkin Fulanin Legas, Alhaji Muhammadu Bambado ya shaida wa Aminiya cewa ba su da masaniya bisa sabuwar rijistar da ake yayatawa za a fara yi wa Fulani a Kurmi. Shi ma mataimakin shugaban kungiyar, Alhaji Salisu Garba Bashankai, ya shaida mana cewa ba su da […]
Shugaban majalisar sarakunan Fulani mazauna jihohin Kudu maso yamma kuma sarkin Fulanin Legas, Alhaji Muhammadu Bambado ya shaida wa Aminiya cewa ba su da masaniya bisa sabuwar rijistar da ake yayatawa za a fara yi wa Fulani a Kurmi. Shi ma mataimakin shugaban kungiyar, Alhaji Salisu Garba Bashankai, ya shaida mana cewa ba su da labarin sabuwar rijistar da ake magana.
A nasa bangaren, shugaban kungiyar Miyatti Allah reshen Jihar Ondo, Alhaji Bello Garba cewa ya yi a daman can suna da rijista wadda kungiyarsu ke yi wa daukacin mambobinsu a matakin kowace jiha kuma da yawansu na da wannan rijistar. Yayi kira ga wadanda ba su da ita da su yi kokari su yi. Ya kuma ce za su iya yin kowace irin rijista domin ingantuwar tsaro, matukar ba ta saba wa dokar kasa ba.
Yawancin shuwagabannin Fulanin ba su gamsu da tsarin sabuwar rijistar da ake ta cece-kuce a kanta ba, domin a cewarsu hakan wani launin wariya ne kawai, kana da yawansu na ikirarin rashin masaniya a kanta, domin a cewarsu, sama da kaso sittin na shuwagabannin ma ba su da masaniya a kan sabuwar rijistar.
Shugaban kungiyar hadin kan ’yan Arewa (ACF), Alhaji Ado dansudu, ya ce akwai bukatar sanin kungiyar da ta fito da sabuwar rijistar? “Abu mafi mahinmanci shi ne kawai a fahimci juna a sami zaman lafiya. Matsalolin Fulani makiyaya da manoma, ana samun su a ko’ina a duniya kuma ana bin hanyoyin da suka dace wajen warware su. Duk inda ka ji an ce noma, za ka ji an ce kiwo. Don haka Allah ne Ya hallice su tare kuma dukkaninsu hanyoyi ne na cin abinci. Don haka in mutane suka kasa magance matsalar hanyoyin cin abincinsu, suka soma kashe-kashe a haka, to sun zama dabbobi ke nan. Su ma Fulanin akwai nasu koke-koken, sau da yawa ana far masu, a kashe su, a kora shanunsu. Saboda haka shawarata ita ce, duk masu ruwa da tsaki a wannan lamarin su hadu su samar da mafita. Idan kungiyar ’yan banga za su yi a tsakanin Fulanin da manoma, sai a yi domin ingantuwar tsaro,” inji shi.