Shugabannin Hausawa sun fara gyara wa fitsararru zama

Sun zagaya sassan Unguwar Sabo mazaunin Hausawa don gyara wa ’ya’yansu zama

Shugabannin Hausawa sun fara gyara wa fitsararru zama

Hakimai da dattawa a Masarautar Hausawan Ibadan sun zagaya sassan Unguwar Sabo mazaunin Hausawa don gyara wa ’ya’yansu zama da kawar da bata-gari daga cikinsu.

Masarautar da hadin gwiwar wakilan kungiyoyin iyaye da ’yan kasuwa sun dauki matakin ne saboda yadda wadansu matasan Hausawa suka mayar da unguwar mashayar miyagun kwayoyi ko maboyar ’yan fashi da suke bata sunan unguwar a idon duniya.

An gudanar da zagayen unguwar ce tare da wakilin Aminiya wanda ya ce, Jarman Ibadan, Alhaji Danjuma Yakubu ne ya jagoranci ayarin wanda ya ziyarci wuraren da ake zargin matasan suna amfani da su wajen aikata miyagun ayyuka a cikin unguwar.

Alhaji Danjuma Yakubu ya shaida wa Aminiya cewa, “Mahukunta a Jihar Oyo suna sane da matakin da muka dauka wanda Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Dahiru Zungeru ya ba mu umarnin tsabtace unguwar daga bata-gari.

“Dalili ke nan da dukkan hakimai da iyaye da masu ruwa-da-tsaki a Masarautar Hausawan Ibadan muka fito don jan kunne da nasiha ga wadannan matasa su yi wa kansu kiyamullaili su nemi ayyuka da sana’a ko mu dauki matakin ladabtarwa ta hanyar gurfanar da su gaban kotu.”

Aminiya ta gane wa idanunta a ranar Asabar din, yadda ayarin hakiman ya fara ladabtar da wadansu matasan Hausawa masu kitso ko tara suma inda aka umarci wanzamai su yi masu askin tal-kwabo nan take.

Biyu daga cikin matasan ’ya’yan wadansu hakiman ne, kuma an yi musu bulala bayan aske, gashin. Matasan da aka ladabtar sun yi nadamar halin da aka same su a ciki.

Daya daga cikinsu da aka sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, “Wallahi na yi nadamar kasancewa a cikin wannan hali, ku taimaka min da addu’a Allah Ya yi min magani, domin akwai abokaina da yanzu haka suke neman aure saboda sun kame kansu ba su shigo cikinmu ba.”

Jarman Ibadan, Alhaji Danjuma Yakubu ya ce “Mun fara bulala a kan ’ya’yanmu ne domin sauran jama’a su gane cewa ’ya’yan shugabanni ma ba su tsira ba balle ’ya’yan talakawa a yayin gudanar da aikinmu na ba-sani-ba-sabo.”

Bincike ya gano cewa, yanzu haka akwai shaguna da rumfuna masu yawa a unguwar ta Sabo da ake fakewa da sayar da magani alhali ba haka lamarin yake ba, miyagun kwayoyi ake sayarwa ga matasa maza da mata da matan aure.

Alhaji Danjuma Yakubu ya ce, “Akwai kwamitin amintattu da muka kafa domin bincikar batun maboyar makamai musamman a wannan lokaci na tabarbarewar tsaro a kasa wanda ya kamata mu bayar da gudunmawarmu a kan wannan matsala da ta shafi kasarmu.”

“Muna gargadin dukkan masu shagunan sayar da magani su cire hannu daga shigo da miyagun kwayoyi cikin unguwarmu domin za mu yi fito-na-fito da irin wadannan mutane da su kansu masu shan kwayoyin domin tsaftace gari.

“Mun samu hadin kai daga sauran jama’ar gari wadanda suka yi mana alkawarin sanar da mu labaran sirri da zai kai mu ga nasara,” inji shi.

Wani Bayarbe mai kula da wani otel mai suna Cif Abdullatif Ajasa mai shekara 60 da ya yi kuruciya a Unguwar Sabo ya shaida wa Aminiya cewa, “Akwai matasa ’yan kasashen Nijar da Ghana da Togo da Benin da Mali da suke haduwa da matasan Hausawa da na Yarbawa wajen aikata fashi da makami.

“Amma abin bakin ciki shi ne sau da yawa muna kama matasan Hausawa da zargin aikata miyagun ayyuka muna mika su ga Sarkin Hausawa, amma sai ka ga wadansu iyayen yara da shugabanni suna zagayawa ta bayan gida domin kamun kafa don a saki ’ya’yansu ba tare da hukunta su ba.

“Muddin irin wadannan iyaye da shugabanni suka ci gaba da irin wannan to kuwa zai yi wuyar gaske hakiman su yi nasara.”

A kwanakin baya Gwamnatin Jihar Oyo ta tura jami’an tsaro zuwa ’yan Bola na Unguwar Sabo wato matsugunin nakasassun da ke fakewa da baracebarace suna aikata ayyukan masha’a.

A wani bincike a wancan lokaci an gano maboyar manyan makamai a matsugunin da yadda ake hada baki da wadansu nakasassun wajen aikata miyagun ayyuka.

Hakan ne ya sa gwamnatin daukar matakin korar dukkan mazauna wurin da kebe wa nakasassun sabon matsuguni a kauyen Akinyele, amma bayan wata biyu suka sake komawa tsohon matsuguninsu na Sabo.

Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa, Unguwar Sabo ta zama wani dandalin sayar da kayan sata da manyan barayi a ciki da wajen Ibadan suke amfani da ita wajen sheke ayarsu.

Hakan ne ya sa sabon Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ali Dahiru Zungeru daukar matakin tsaftace unguwar daga bata-garin ta hanyar gano maboyarsu da kama su tare da mika su ga jami’an tsaro domin hukunta su.