Shugabannin jami’o’i da NUC sun shaida wa kwamitin Majalisar Dattijai babu jami’ar da ta qara kuxin makaranta a Najeriya
Babu wata jami’a a Najeriya da ke qarvan kuxin makarantar na (tuition) ballantana ma ace wai an qara kuxin kamar yadda ake yaxa wa kamar yadda Sshugaban Hukumar kula da jam’o’in Najeriya farfesa Abubakar Adamu Rasheed ne sanar. Shugaban hukumar, wanda ya yi magana a madadin jami’o’i 40 na gwamnatin tarayya a gaban kwamitin kula […]
Babu wata jami’a a Najeriya da ke qarvan kuxin makarantar na (tuition) ballantana ma ace wai an qara kuxin kamar yadda ake yaxa wa kamar yadda Sshugaban Hukumar kula da jam’o’in Najeriya farfesa Abubakar Adamu Rasheed ne sanar.
Shugaban hukumar, wanda ya yi magana a madadin jami’o’i 40 na gwamnatin tarayya a gaban kwamitin kula da jami’o’i da bayar da tallafin karatu (TETFUND) na majalisar Dattawa ya ce babu qanshin gaskiya a maganar cewa an qara kuxin makaranta.
Ya ce maganar ta taso ne a daidai lokacin da jami’o’in ke tsakiyar karatu, wanda ke nuni da lokacin da bai yi daidai da lokacin da za a iya qara kuxin makaranta ba.
Farfesa Rasheed wanda ya samu rakiyar wasu daga cikin shugabannin jami’o’in da aka ambata cewa sun qara kuxin ya ce banda kuxin gyare-gyaren xakunan bincike da sauran ayyuka da ake qarva daga xalibai, babu wani kuxi da ake karva.
“Mun yi matuqar damuwa da ganin labarin. Labarin ya fara ne daga kafafen yaxa kabarai na zamani na yanar gizo, mun tuntuvi qungiyar malamai ta ASUU inda su ka ce ba su da masaniya. Babu wanda ya yi wannan maganar. Labarin na da ruxar wa domin jami’o’i suna tsakiyar karatu ne yanzu.
“Kuma idan ka duba jerin jami’o’in da aka lissafa, za ka ga akwai jami’o’in gwamnatin tarayya, na jihohi da masu zaman kansu. Na nemi shugabannin jami’o’in amma duk sun ce ba su da masaniya a kan labarin.
Wasu daga ciki sun ce suna qarvan daga naira dubu 3 zuwa dubu 4 daga xaliban kimiyya, amma ba su da yawa. Ina mai tabbatar muku da cewa wannan labarin bai da asali. Babu jami’ar da ta qara kuxi, kuma yadda aka haxa jami’o’in gwamnatin tarayya, da na jihohi da masu zaman kansu, ka san labarin bai da wata ma’ana,” kamar yadda ya sanar da kwamitin.
Tun farko dai shugaban kwamitin, Sanata Barau Jibrin ya sanar da hukumar NUC da shugabannin jami’o’in cewa an kira taron ne domin labarin da suka samu cewa an qara kuxin makaranta da kuma koken qarancin kuxi da jami’o’in ke samu.
Ya ce Majalisar Dattawa ta tattauna matuqa a kan matsalar qarancin kuxin wanda jami’o’in ke yawan magana akai, sannan kuma za su yi aikin tare da hukumar NUC da shugabannin jami’o’i da kuma kwamitin su domin kawo qarshen koken a kasafin kuxi na nan gaba.
Dukkan membobin kwamitin da suka halarci taron sun bayar da ta su gudunmuwar, sannan kuma suka yi jawabi akan tavarbarewar ilimi, musamman na jami’o’in qasar nan.
Sanata Magnus Abe, Yahaya Abdullahi, Tijjani Kaura, Oluremi Tinubu da Foster Ogola sun buqaci Hukumar NUC ta yi qoqari wajen dawo da martabar jami’o’in Najeriya, inda Sanata Abdullahi ya kwatanta ilimi a matsayin “Abu ma fi tsada a duniya.”
Sanatocin, wanda suka yarda da cewa gwamnati ta cire hannun ta kacokan kan kuxin makaranta, sun ce “Babu wata qasa a duniya da ke bayar da karatu kyauta har da qasar Chana. Dole mu faxa wa kan mu gaskiya. Magana ce ta jami’o’in Najeriya, kuma tambayar ita ce yaya za yi a samu gyara?”