Shugabannin jam’iyyar APC na Legas sun taya Aregbesola murna
daukacin shugabanni da ’yan jam’iyyar APC da ke Jihar Legas sun taya Gwamna Rauf Aregbesola murnar lashe zaben Jihar Osun inda ya sake darewa kujerar gwamanan jihar a karo na biyu.Tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar, Sanata Bola Ahmed Tunubu ya bayyana nasarar da Aregbesola ya samu da jajircewar da ya yi duk […]
daukacin shugabanni da ’yan jam’iyyar APC da ke Jihar Legas sun taya Gwamna Rauf Aregbesola murnar lashe zaben Jihar Osun inda ya sake darewa kujerar gwamanan jihar a karo na biyu.
Tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar, Sanata Bola Ahmed Tunubu ya bayyana nasarar da Aregbesola ya samu da jajircewar da ya yi duk da kalubalen da ya fuskanta daga jam’iyyar PDP.
Ya ce, “Nasarar da ka samu ta zo ne saboda tsayawar da ka yi, kai da fata, wajen ganin ka fuskanci dukkan kalubalen da ke gabanka, musamman ma kalubalen da masu son kwace mulki da karfin tuwo, wato jam’iyyar PDP, suka yi maka. Mun yaba da kokarinka kuma mun jinjina maka a matsayinmu na ’yan jam’iyyar APC a kasa baki daya”.
Shi ma Alhaji Garba Chede, daya daga cikin shugabannin jam’iyyar APC, bangaren ’yan Arewa, cewa ya yi, “Aregbesola ya nuna wa PDP ba ta da tasiri kuma duk da irin matakan da suka dauka na juya zaben, mun yi nasara a kansu. Osun ba Ekiti ba ce kuma muna fata Allah Ya maimaita mana nasarar a Jihar Legas”.
Shi ma Malam Muhammad Iliya cewa ya yi, “Gaskiya mun yi nasara kuma muna gode wa Allah da Ya ba mu nasara. Babu shakka zaben da aka yi ya nuna cewa karshen jam’iyyar PDP ya zo a kasar nan. Saboda haka muna taya Aregbosola murna. Muna addu’ar Allah Ya taya shi riko ya ci gaba da ayyukan alherin da yake yi wa jama’ar Osun”.