Shugabannin kananan hukumomi sun nemi Gwamnan Kebbi ya sakar musu mara
Shugabannin kananan hukumomin Jihar Kebbi sun bukaci Gwamnan Jihar Alhaji Sa’idu Usman Nasamu dakingari ya sakar masu kudadensu da suke samu daga kason tarayya.Wannan kiran ya fito ne daga bakin Shugaban karamar Hukumar Birnin Kebbi Alhaji Musa Ibrahim dan Illela, kuma shugaban kungiyar Shugabannin kananan Hukumomi (ALGON), reshen jihar a lokacin da suka kai gaisuwa […]
Shugabannin kananan hukumomin Jihar Kebbi sun bukaci Gwamnan Jihar Alhaji Sa’idu Usman Nasamu dakingari ya sakar masu kudadensu da suke samu daga kason tarayya.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin Shugaban karamar Hukumar Birnin Kebbi Alhaji Musa Ibrahim dan Illela, kuma shugaban kungiyar Shugabannin kananan Hukumomi (ALGON), reshen jihar a lokacin da suka kai gaisuwa ga Gwamna Sa’idu dakingari a gidan gwamnatin jihar.
Shugabannin sun ce lokaci ya gabato da Gwamna Sa’idu dakingari zai kara ba da kaimi domin dada inganta rayuwar al’ummar jihar, musamman ganin yadda siyasa za ta fara nan ba da dadewa ba. Ya ce koda yake Gwamnan ya aiwatar da ayyukan raya kasa a duk fadin jihar, su ma shugabannin kananan hukumomi idan aka sakar musu kudinsu akwai gaggarumar rawar da za su taka ta fannin kyautata wa al’ummarsu kafin wa’adin mulkinsu ya cika.
Ya roki Gwamnan da idan zai kawo musu dan takaran Gwamna a jihar, to ya kawo wanda jama’a ke so, mutumin kirki wanda ya san siyasa ya kuma san ’yan siyasa mai mutunci da zai dora daga inda Gwamna dakingari ya tsaya.
Da yake maida jawabi Gwamnan dakingari ya ce idan har akwai kudi a asusun hadin gwiwa a tsakanin kananan hukumomi za a ba su, kuma ya ce duk irin mukamin da jama’arsa suka neme shi ya zo ya yi takara koda na kansila ne zai yi da yardar Allah, amma su bar wa Allah komai sai lokaci ya yi.