Shugabannin makarantun sakandare sun ziyarci Aminiya a Ibadan
A makon jiya ne kungiyar Shugabannin Malaman makarantun sakandare ta kasa (ANCOPSS), ta kammala babban taro na 57 da ta saba yi a kowace shekara a birnin Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo. Wakilan kungiyar daga jihohi 36 har da Abuja ne suka halarci taron da aka gudanar cikin kwanaki hudu.Shugabannin makarantun, wadanda suka fito daga Jihar […]
A makon jiya ne kungiyar Shugabannin Malaman makarantun sakandare ta kasa (ANCOPSS), ta kammala babban taro na 57 da ta saba yi a kowace shekara a birnin Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo. Wakilan kungiyar daga jihohi 36 har da Abuja ne suka halarci taron da aka gudanar cikin kwanaki hudu.
Shugabannin makarantun, wadanda suka fito daga Jihar Kano, sun kai ziyara ofishin Jaridar Aminiya, da ke unguwar Sabo, a birnin Ibadan. Shugaban makarantar sakandare ta Damargu, kuma shugaban ANCOPSS na yankin Bichi, Alhaji Ibrahim Sadik Bichi da sakataren kungiya na yankin Gwarzo, kuma shugaban makarantar sakandare ta ’yan mata da ke Gwarzo, Alhaji Awwalu Bello Sani Gwarzo, su ne suka jagoranci takwarorinsu.
Da yake maraba da bakin nasa, wakilinmu ya yi musu bayanin yadda jaridar Aminiya ta samu karbuwa kuma ta yi fice a tsakanin masu karanta ta da suka hada da kabilun Yarbawa da jami’an tsaro da al’ummar Hausawa da ke zaune a sashen Kudu maso Yamma.
Wakilinmu ya shaida wa bakin cewa, “Jaridar Aminiya, ta samu karbuwa ne a dalilin ingatattun labaran da take fayyace gaskiyar aukuwarsu a cikin shafukanta a kowane mako, kan al’amuran da suka shafi halin da kasa ke ciki da siyasa da koke koken jama’a da labaran abubuwan tausayi da mamaki da ban haushi da labaran kungiyoyi da sana’o’i da dandalin nishadi da wasanni da labarai a kan kiwon lafiya da shafin kwalliya da adon mata da girke-girken abinci da shafi da aka kebe sukutum domin wa’azin addinin musulunci da kirista da Mumbarin Musulunci, har da shafin kimiyya da kere kere da Adabi da labaran kasashen duniya da wakilan Aminiya, suke samowa daga sassa daban daban a ciki da wajen Najeriya.”
Shugabannin makarantun na Damargu da Gwarzo Alhaji Ibrahim S. Bichi da Barrister Awalu Bello S. Gwarzo, su ne suka yi jawabai a madadin abokanan aikin nasu. Sun ce, “irin labaran da suka shafi ‘yan uwanmu da ke zaune a wannan sashe da muke karantawa a cikin jaridar da sauran muhimman labarai, su ne yasa muka yanke shawarar neman ofishin wannan jarida a Ibadan, domin samun karin haske a kan abubuwa daban-daban da suka shafi jaridar.
“Mun yi matukar farin ciki da jin muhimman bayanai da suka shafi hanyoyin samo labarai da kuke bi domin fadin gaskiya ta tsarkake labarai kafin a buga su a cikin shafukan jaridarku,” inji shi.
Dangane da taronsu sun bayyana cewa:”A matsayin Jihar Kano tumbin giwa, ita ce ta aiko da shugabannin makarantu 165 da suka zarce yawan kowace jiha a wajen wannan taro da muka tattauna a game da matsalolin da suka dabaibaye ci gaban ilmi a kasar nan musamman irin tallafin da makarantu suke samu daga gwamnatocin jihohi wanda ya yi kadan matuka. Tawagar shugabannin sun yi amfani da wannan dama wajen ziyarar wurare daban daban da al’ummar Hausawa suke gudanar da harkokinsu na yau da gobe a Ibadan.