Shugabannin PDP na Arewa sun bukaci Fayose ya ajiye neman shugaban qasa
Shugabannin Arewa na jam’iyyar PDP jiya sun bukaci Gwamna Ayo Fayose na jihar Ekiti ya mutunta tsarin karba-karba na jam’iyyar ya janye shirinsa na neman takarar shugabancin kasar a zaben 2019. Shugabannin jam’iyyar sun ce Arewa na da dimbin mutanen da suka dace su tsaya takara saboda haka suka gargadi gwamnan kada ya yi jayayya […]

Shugabannin Arewa na jam’iyyar PDP jiya sun bukaci Gwamna Ayo Fayose na jihar Ekiti ya mutunta tsarin karba-karba na jam’iyyar ya janye shirinsa na neman takarar shugabancin kasar a zaben 2019.
Shugabannin jam’iyyar sun ce Arewa na da dimbin mutanen da suka dace su tsaya takara saboda haka suka gargadi gwamnan kada ya yi jayayya da tsarin karba-karba na jam’iyyar.
Fayose wanda daga yankin Kudu ya fito ya bayyana aniyarsa ta neman tsayawa takarar shugaban kasar karkashinjam’iyyar PDP duk da cewa jam’iyyar ta tsara dan takarar zai fito daga yankin Arewa ne.